An Ci Tarar Sojan Da Ya Ci Zarafin ‘Yar Fim a Fatakwal

0
1027

MUSA MUHD.KUTAMA, Daga Fatakwal

RUNDUNAR Soja ta 6 da ke Fatakwal Jihar Ribas ta sanar da daure wani soja mai suna Suleiman Olamilekan na tsawon sa\’o\’i ashirin da hudu saboda samunsa da zargin cin zarafin wata ‘yar wasan fina-finan Nollywood mai suna Ebere Ohakwe.

Mai Magana da yawun rundunar ta  6, da ke birnin Fatakwal Kanar Aminu Iliyasu ne ya sanar da haka Alhamis ya ce baya ga hukuncin daurin na kwana daya kurtun sojan zai “rasa albashinsa na wata guda laifin da ake zargin sojan da aikatawa na cin zarafin ‘yar wasan fim din ya saba dokar aikin soja”.Kanar Iliyasu ya ci gaba da cewa rundunar sashen ladaftarwa na rundunar sojan ta samu Suleiman Olamilekan da laifin da ake zarginsa da aikatawa kuma ta hukunta shi.

Karkashin umarnin Enobong Udoh kwamandan sojan runduna ta 6 .

 

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here