Gobara Ta Kone Mutum Biyu A Delta

0
1410

MUSA MUHAMMAD KUTAMA, Daga Kalaba

WATA gobara da aka yi a garin  Udu, da ke  karamar hukumar Udu yankin Warri jihar Delta ta lakume rayukan wasu yara biyu masu suna Ebenezer da Eliot ‘ya’yan wani mutum mai suna Mista Blessing.Duk kanin kokari da jama’ar unguwa suka yi na ganin sun kashe gobarar kafin zuwan jami’an kashe gobara gidan da abin ya faru ya ci tura.

Wata majiya ta shaida wa wakilinmu  cewa musabbabin gobarar “kyandir ne mai gidan ya kunna kuma aka dora shi a kan robar fenti suka kwanta barci har kyandir din ya kone  ya narke ita ma robar ta narke ta kama wuta sanadin haka sai makwabta suka ga hayaki na tashi a dakin shi kuma maigidan Mista Blessing yana ciki shi da yaran suna barci aka jiwo yana ihun a zo a cece su ko da makwabta suka garzayo hayaki ya riga ya turnike ko ina yaran kuma aka ji suna ihu suna kuka suna ambaton a cece su mamayewar da hayakin ya yi ko ta ina ne ya sanya aka kasa gane takamaimai inda kofar dakin take bare ma a shiga  a ceto mutanne da ke ciki”.

Haka nan kuma an ce koda jama’a suka yi galabar fasa dakin ta makwabta suka shiga “an riga an tarar yaran wutar ta kone su kurmus sun yi kamar gawayi” .inji majiyar gidaje sama da hudu ne aka kiyasta sanadin wannan gobara suka kone.Dukiya kuwa da kadarori na milyoyin kudi a gidan hudu aka yi asara.

Shi kuma mai gidan Blessing an garzaya asibiti da shi nan garin Warri idan yana da sauran shan ruwa a ceto shi ya zuwa rubuta wannan labari idan banda yara biyu Ebenezer da ‘yar uwarsa Eliiot da gobarar ta ci babu wata asarar rayuka da aka samu sai fa ta dukiyoyi.

Oweh  Alex, jami,in kashe gobara ya shaida wa manerma labarai cewa yaran biyu sun riga sun kone kafin zuwan su amma duk da haka sun yi bakin kokari wajen kashe wutar da ta ci gidaje hudu har da  gidan da yaran suka kone wanda shi ne sanadin gobarar inji shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here