GWAMNA EL-RUFAI YAYI TANKADE DA RAIRAYA A GWAMNATINSA

0
973

Daga Usman Nasidi

GWAMNAN Jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai ya mika sunayen sababbin kwamishinoni majalisar dokokin jihar domin tantancewa.

An nada wasu sababbin manyan sakatarori a ma’aikatun jihar inda aka sauya wa wadansu daga cikin wadanda suke kai aka can canza musu ma’aikatu.

Wadanda aka kai sunayen su majalisar jihar domin tantance wa sun hada da Kabiru Mato a matsayin kwamishinan Ayyukan Gona, Umma Hikima, kwamishinan Shari’a, Hafsat Baba, kwamishinan Harkokin Mata da Ja’afaru Sani a matsayin kwamishinan kananan hukumomi.

Wadansu manyan sakatarori biyar sun yi murabus.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here