Kananzir Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Wani Yaro A Benin

0
957

MUSA MUHD.KUTAMA, Daga  Kalaba

WATA mata  mai suna Ata Buhari ta kashe danta bisa kuskuren shayar da shi ruwa ta ba shi kananzir ya sha wanda hakan ya yi sanadiyyar mutuwar yaron dan wata goma sha takwas da haihuwa.

Wannan lamari ya faru ne a layin Iganmu da ke  birnin Benin hedkwatar  Jihar Edo.Yadda abin ya faru kamar yadda wannan jarida  ta samu labari an ce yaron ne kishirwa ta kama shi yana ta kuka yana ambaton ruwa zai sha ita kuma uwar cikin hanzari ta tafi ta dauko ruwa don  ta ba shi ashe ba ta san cewa kananzir ba ne a ciki ba ruwa ba ne.

Majiyar labarin mu  ta ci gaba da cewa kakaro kanazir din da yaron ya yi ne wanda ya rage na bakinsa bai hadiye ba shi ba ne, aka ce uwar ta gane cewa ashe ba ruwa ba ne ta ba shi, daga nan fa sai ido ya raina fata ta garzaya kantin sayar da magunguna domin a kawo mata dauki a ba ta maganin da zai karya karfin kananzir da yaron ya riga ya sha.

Uwar yaron da take yi wa manema labarai karin haske game da tsautsayin da ya same ta, ta shaida wa ‘yan jarida cewa daya daga cikin dan su ya je ya zuba ruwa a cikin jarka da suke kai wa shago suna kasuwanci ji take yi bai dauki jarkar ruwan ya tafi da ita shago ba sai ta tsiyayo ruwan kananzir din ta ba yaron ba tare da ta sanin ba shi  kuma ya sha har sai da  ya kai ga  kakaro ragowar na bakinsa da bai riga ya wuce masa ciki ba.inji uwar yaron .Shi ma Malam Buhari Hassan mahaifin yaro ya ce ba ya gida hakan ta faru sai dai kira ya ji a wayarsa ta hannu an ce ya zo asibiti ana kiransa zuwan sa can Asibiti ke da wuya ya ce sai aka mika masa gawar dan nasa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here