MUSA MUHAMMAD KUTAMA Dag a kalaba
DIREBOBIN da ke dakon kaya daga sassan Arewacin Nijeriya zuwa na Kudanci sun koka da halin tasku da gasa masu aya a hannu da jami’an tsaro da ke yin sintiri a kan manyan hanyoyin ke yi .Da yake koka wa wakilinmu na kudanci ta wayar salula matsalar, mai magana da yawun direbobin, Alhaji Muhammad Lawal Saminaka ya ce a koda yaushe suka dauko kaya daga Arewa zuwa wasu daga cikin jihohin Akwa Ibom da Ribas ko kuma Kuros Riba suna shan matsi daga hannun jami’an tsaro da ke yin sintiri a kan wadannan hanyoyi.” Suna karbar kudi a hannunmu kowane shinge ka je Naira Dubu za ka ba su ko kuma Naira Dubu biyu, idan direba bai bayar ba a doke shi a yi masa wulakanci ko su yi wa direba ma gashin kuma”inji shi.
Alhaji Lawal saminaka direban babbar mota ya ci gaba da cewa “ka ga a kan ban ba su kudin da suka kayyade min ba dubi irin yadda suka doke ni har sai da jini ya taru a gefen idona”.Da aka tambayi direban ko wadanne jami’an tsaro ne suke yi masu wannan wulakanci da yake kokawa a kai sai ya ce “shingayen akwai na sojoji, akwai na ‘yan sanda akwai kuma na ‘yan karbar haraji kowane shinge ka je kowa da irin kudin da zai ce ka ba shi idan ka kiya kuma jiki ya yi tsami”.
Har wa yau ,direban ya koka da yadda idan sun yi dakon kaya kudin da ake biyansu ba su isar su,ga shi za su sayi mai “muna kashe fiye da Naira Dubu 150 a kan hanya bai wa jami’an tsaro da kuma ‘yan rabanu wanda kudin dakon kaya da mutum ya yi idan baI yi hatatra ba za su kare a wurin raba wa ma’aikata”.
Alhaji Muhammadu Lawal Saminaka ya kara da cewa babu wani abu da direba zai yi a halin yanzu matukar dai zai bi manyan hanyoyin Nijeriya daga Arewa zuwa Kudanci har sai ta tanadi kudaden da zai raba wa ma’aikata da kuma masu karbar haraji lamarin da ya ce yana kawo tarnaki da kuma mayar da hannun agogo baya wajen yaki da cin hanci da rashawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari yake yi a halin yanzu.
Karshe ya yi kira ga shugabannin jami’an tsaron da na masu karbar kudaden shiga na gwamnati da su yi wa maaikatan su fada su daina gallaza wa direbobi masu dakon kaya suna mayar da su saniyar tatsa.