nan ta ADP a jihar Filato kuma shi ne shugaban kamfanin buga mujallar
nan ta Newsgate da ake bugawa a garin Jos.
A wannan tattaunawa da ya yi da wakilinmu ya bayyana shirin da wannan
sabuwar jam\’iyya ta ADP tayi, na karbe mulkin Nijeriya daga jam\’iyyar
APC.
Ga yadda tattaunawar ta kasance
GTK; Mane ne manufofin wannan sabuwar jam\’iyya ta ADP?
Nanyah; Ita dai wannan sabuwar jam\’iyya ta ADP, wadda wasu masu
kishin kasa da suka haxa da matasa da waxanda basu taba rike wasu
mukamai ba ne suka hadu suka kafa ta.
Kuma babbar manufar wannan jam\’iyya shi ne ceto al\’ummar Nijeriya daga
irin mawuyacin halin da suke ciki, musamman kan tashi komai na
harkokin rayuwa a Nijeriya.
Idan wannan sabuwar jam\’iyya ta ADP ta karvi mulkin Nijeriya, zata yi
amfani da tsarin tattalin arzikin da zai fito damu daga cikin wannan
mawuyacin hali da muke ciki.
Kuma a tsarin wannan jam\’iyya muna son mu yi amfani da tsarin zaben
A4, a dukkan zabubbukan da zamu yi. Wato tsarin mutum ya tsaya zabe
mutanen da suke sonsa su layi su bi bayansa su zabe shi. Babu ruwanmu
da tsarin zaben wakilai.
Idan kana da farin jini a kauyenka ko a garinka ko a jihar ka, sai
ka fito ka tsaya mutane suyi layi, su zabeka. Babu ruwanmu da tsarin a
kawo wasu mutane wadanda zasu wakilci jama\’a daga wata karamar hukuma
ko jiha ko wani gari. Duk \’yan jam\’iyyar nan ne zasu tsaya su zabi
wanda suke so.
Haka zamu a zaben shugabannin jam\’iyya da zabubbukan \’yan takarar mu
a matakan zaben shugabannin kananan hukumomi da gwamnonin jihohi da
\’yan majalisunsu da zaben \’yan majalisun tarayya da shugaban kasa,
duk haka zamu yi. Domin muna son mu tsayar da mutanen da jama\’a suke
so.
GTK; Maye banbancin wannan sabuwar jam\’iyya ta ADP da jam\’iyyun PDP da APC?
Nanyah; Ita dai wannan sabuwar jam\’iyya ta ADP kamar yadda na fada
wadansu masu kishin kasar nan ne suka hadu suka kafa ta. Kuma wannan
sabuwar jam\’iyya ta kowa da kowa ce.
Amma kaga jam\’iyyun PDP da APC jam\’iyyu ne na masu kudi da wadanda
suka dade suna rike da mukamai iri daban daban a Nijeriya. Sune ne
suka taru suka kafa su, sune shekaranjiya sune jiya sune kuma yau.
Irin mutanen da waxannan jam\’iyyu na PDP da APC ke nan suka kunsa.
GTK; Kana ganin wannan jam\’iyya zata iya karvar gwamnatin Nijeriya
daga jam\’iyyar APC?
Nanyah; Babu shakka bisa dukkan alamu wannan sabuwar jam\’iyya, zata
iya qarvar mulkin Nijeriya daga jam\’iyyar APC. Domin Akwai fitattun
\’yan siyasa da suke son shigowa wannan sabuwar jam\’iyya kamar tsohon
mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar da tsohon shugaban
kasa Olusegun Obasanjo da tsohon Shugaban kasa Janar Babangida da
tsohon shugaban kasa Abdulsalam Abubakar da gwamnonin jihohi masu ci
guda 16 da Sanatoci masu ci guda 32 da \’yan majalisar wakilai guda 148
duk suna nan suna shirin dawowa wannan sabuwar jam\’iyya ta ADP. Don
haka muna ganin wannan jam\’iyya zata mamaye kasar nan, ta karve mulki
a zaven shekara ta 2019.
GTK; Daga lokacin da kuka kawo wannan jam\’iyya nan jihar Filato, zuwa
yanzu yaya kaga yadda al\’ummar jihar suka karvi wannan jam\’iyya?
Nanyah; Daga lokacin da muka kawo wannan jam\’iyya nan jihar Filato
zuwa yanzu al\’ummar jihar nan sun fito sun rungume ta. A yanzu duk
inda ka shiga a jihar nan zaka ji ana maganar wannan sabuwar jam\’iyya.
Domin mutanen jihar nan sun gaji da jam\’iyyun PDP da APC. Duk
qanannan hukumomin jihar nan 17 mun riga mun kafa shugabannin riko. A
ko\’ina a jihar nan ana nan ana ta yin rijistar \’yayan wannan jam\’iyya.
GTK; Maye zaka ce kan kara lokacin shugabannin kananan hukumomi da
gwamnan jihar Filato ya yi?
Nanyah; Abin da yasa gwamna Lalong ya yi wannan karin lokaci na
watanni 6 ga shugabannin qananan hukumomi, ya sanya an yi masa
bincike ne a kananan hukumomin jihar nan 17. Wannan bincike ya nuna
masa cewa idan ya yi zaben nan a yanzu, da kyar zai iya cin kananan
hukumomi guda 5. Don haka ya yi wannan karin lokaci don ya yi wasu
abubuwan da zasu farantawa jama\’a rai. Amma ina mai tabbatar maka ko
maye gwamna Lalong ya yi ba zai sami nasara ba. Domin babu abin da ya
yiwa jihar nan.
Maganar biyan albashin da ya yi ba Buhari ne ya bashi kudin biyan
albashin ba? Ana bin jihar nan bashi sama da naira biliyan 100 amma
babu wanda aka baiwa ko kwabo a cikin wadanda suke bin jihar nan
bashi. Alhalin an yi yarjejeniya da shi cewar wadannan kudade da
shugaban kasa Buhari ya baiwa gwamnoni kashi 50 su biya albashi kashi
50 kuma su biya basussuka amma gwamna Lalong bai biya bashin ko kwabo
a cikin wadannan kudade ba.
Babu abin da gwamna Lalong ya yi a jihar nan, sai yawace yawace da
kashe kudaden jihar nan. Ana daukar hayar jirgi don kai \’yarsa
makaranta a Yola aje a dawo da ita. Alhalin mutane suna mutuwa a
asibitoci saboda rashin magunguna. Hanyoyi babu gyara don haka muna da
karvin gwiwar karve gwamnatin jihar Filato daga APC.