Daga Usman Nasidi
WATA kungiyar \’yan fafutuka mai suna, National Rebirth Group (NRG), tace tana shirin yin wata zanga-zangan mutane miliyan 1 akan samarwan tattalin arzikin gwamnatin tarayya, wanda ke shafan rayukan mutane.
Kungiyar ta bayyana hakan ne a wata jawabin da shugabanta ya rattaba hannu, Salisu Mohammed a ranan Alhamis.
A cewar sa, talaucin da ke cikin kasa, tashin tattalin arziki, da kuma yunwan da mutane ke fama da shi. Saboda haka, zasu gudanar da zanga-zanga domin kira ga gwamnatin tarayya akan farfado da tattalin arzikin Najeriya.
Yace: “Muna kira ga kungiyoyin fafutuka, yan kasuwa, kungiya kwadago, matasa, dalibai, mu hada karfi da karfe wajen kawo karshen wannan talauc.
“ Wajibi ne mu hada hannu domin yakan samarwa gwamnatin tarayya da ke shafan rayukan mutane, mun zabe su ne kuma muna shirye da yaki da su koma mai zai faru ya faru.\”