Idan Gwamnatin Ta Ba Ni Dama Zan Kafa Matatar Mai – Danjuma Ibrahim

0
1215

MUSA MUHAMMAD KUTAMA, Daga Kalaba

WAKILINMU na kudanci  a Kalaba MUSA MUHAMMAD KUTAMA  ya tattauna da dan  kasuwa mai harkokin man fetur wato indifenda mai zaman kansa kan harkokin fataucin man fetur da kuma yadda yake ganin za a warware tare da shawo kan matsalar wahalar man fetur, Alhaji Danjuma Ibrahim Shelleng ya ce idan gwamnati za ta bayar da lasisi ga ‘yan kasuwa masu zaman kansu su kafa matatar man fetur ko ma’adaninsa shi zai yi haka domin tausaya wa masu karamin karfi. Ga yadda tattaunawar ta kasance:-

GTK:Gabatar da kanka ?

Alhaji Danjuma Ibrahim: sunana Alhaji Danjuma Ibrahim  Shelleng ;

GTK: ’Yan Nijeriya  sun rika baza jita-jitar mai yiwuwa gwamnati ta qara farashin albarkatun man fetur,waje daya kuma suna zargin ku ‘yan kasuwa da ba ta isashshiyar damar yin hakan, menene gaskiyar lamarin?

Alhaji  Danjuma Shelleng: Lallai ba gaskiya ba ne gwanati ma na kokarin yadda za ta samu abubuwa su tafi yadda ake so shi yasa ma duk matatun mai da  ake da su taga sun fara aiki .

GTK:Amma ai duk da haka ana kokawa  da irin yadda kanazir ke dada  dan karen tsada baka ganin hakan biri ya so ya yi kama da mutum lura da cewa wasu ma sun koma yin amfani da dusar katako ko itace wajen yin girki shin mai ya kawo tsadar kanazir din ma?

Alhaji Danjuma shelleng: Eh! To gaskiya kasan saboda matsalar canjin takardun kudi abinda ya shafi naira zuwa dala da kuma sauran takardun kudi na kasashen waje shi ya sanya aka samu tsadar kanazir domin su masun shigo da mai kasar nan daga waje suna samun matsalar tsadar farashin Dala, amma duk da haka wannan ba wani  abu ne da zai sanya a ce kanazir ya yi tsada tunda  gwamnati ta tabbatar mana cewa za ta sanya matatun mai da ake da su a kasar sun kama aiki muna sa rai in sha Allahu idan suka fara aiki duk wahalhalun nan za su kau. Misali a yanzu ai ka ga kanazir din farashinsa  ya fadi wanda  a da can  ana sayar da shi kan naira 400 yan zu kuma ya koma naira 250.ko naira 200.saboda mene ne saboda matatun man namu da suke yin aiki kadan-kadan

GTK: Kana ganin cewa idan gwamnati ta mallaka masu lasisin ku  mallaki daffo-daffo na mai wahala da karacin mai a Nijeriya za ta iya zama sai tarihi kusan kowace gwamnati tun daga ta soja zuwa yanzu ta zo sai an smau matsalar ko ta karin farashin albarkatun man feturt ko kuma ta karancinsa?

Alhaji Danjuma Shelleng: Eh! To a gaskiya kam ya kamata gwamnati ta dage ta bayar da lasisin kafa daffo-daffo ga ‘yan kasuwa wanda suma za su iya sayen danyen  mai su tace idan aka yi haka wannan zai taimaka wajen bunkasa yawaitar man nan .

GTK: Kana ganin idan har gwamnatin ta bari kuka kafa ma’ajiyar man fetur farashin mai zai iya daidaituwa ganin cewa wani ka iya boye nasa sai na wasu ya kare ya fito da shi misali kamar irin yadda masu sana’ar hatsi ake zargi suna yi?

Alhaji Danjuma Shelleng:  A’a ba zai kawo haka ba abin da ma zai kawo sai ma farashin ya rika faduwa alal misali yau a ce mutane kalilan haka sun samu lasisi ga gwamnati na yi kamar yadda Dagote shi ma ya ke yi, to gwamnati ta fitar da nata a kasuwa shi ma Dangote ya fitar da nasa a kasuwa a ce kowa ma ya fitar da nasa a kasuwa to ka ga kaya zai yalwanta idan ya yalwanta a lokacin dole zai kawo faduwar farashi.Misali a yanzu haka ma kasuwar da muke yi kasuwar Gas din nan wato dizel za ka ga farashi kowa da irin nasa idan ka je nan za ka ga farashin wancan daban na wannan ma daban da ‘yan kasuwar su ne suke bin masu kaya suna kira su zo su saya .To yanzu masu kayan su ne suke bin ‘yan kasuwa suna cewa ina da kaya kaza ku zo ku saya ka ga yanzu kasuwa ta juya saboda faduwar farashin gas wato dizel.

GTK: Tambayar da masu karatun wannan jarida ke yi ita ce tsakanin ku ‘yan kasuwa da ke hada-hadar man fetur da dangoginsa da kuma gwamnati waye ke da alhakin sanya mai farashin sa ke ta dada hauhawa a wasu lokuta?

Alhaji Danjuma Shelleng: Ai laifin daga dillalan ne dillalan ne ai .

GTK: Na wane bangaren dillalan?

Alhaji Danjuma Shelleng: Na bangaren gwamnati.

GTK: Ko kana da sha’awa  kai ma nan gaba  idan gwamnati ta bayar da  dama kai ma ka  kafa taka ma’ajiyar man fetur?.

Alhaji Danjuma Shelleng: kwarai kuwa domin in da buri kan haka ina son ni ma in saukaka wa talakawa ‘yan uwana da kuma sauran ‘yan Nijeriya wajen wahalar man fetur da dangoginsa ai rashin bayar da dama a ce da gwamnati da ake zargi ba ta yi ne ya sanya haka da irin haka ne kasashe irin su Sin wato China da Indiya suka bunkasa wajen tallafa wa ‘yan kasar su masana’antu.

GTK: Bari ku karkare hirar da wannan tambaya wasu ‘yan Nijeriya na zargin wannan gwamnati ta jan kafa wajen rage wa al’umarta radadin matsin rayuwa da makamantan su yayin da waje daya kuma suke yaba mata musamman yadda ta tilasta ‘yan kasar suka   koma gona gashi yau Nijeriya ce ta biyu a duniya wajen samar da ci maka musamman shinkafa mai Alhaji Shelleng zai ce a nan ?

Alhaji Danjuma Shelleng: Duk wanda ka ga yana sukar wannan gwamnati imma  barawo ne ko azzalumi ne ba mai son ci gaban kasa da na al’ummar ta bane masu kwashe dukiyar kasa ce su arce zuwa wata kasa ta Ketare zuwan wannan gwamanti al’amura sun inganata sun daidatu an samu zaman lafiya an su nasara wajen kawar da ta’addanci boko haram amma duk wannan bai isa a ga kokarin wannan gwmaanti ba an samu nasarar aikin gona manoma bana sun dara ga shi daminar nan ake jira tafadi wadanda suke da burin yin noma sun ma fi na bara yawa saboda alheri da aka samu bana a noma. Kira da zanyi wa ‘yan Nijeriya shi ne su ci gaba da yi wa wannan gwamanti addu’a da fatar alheri shi kuma shugaban kasa Allah ya ba shi lafiya ya dawo ya dora a a aikinsa daga inda ya tsaya .

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here