Babban Limami Ya Goyi Bayan Shawarar Sarkin Kano Sanusi Lamido

  0
  1427

  MUSA MUHAMMAD KUTAMA, Daga Kalaba

  BABBAN limamin barakin soja birged ta 13 Manjo kabiru Yakubu  Sa’ad  shugaban kungiyar Limamai da malamai ta jihar Kuros Riba wato CRS CI&U.Ya yi karin haske game da yadda shawarar da mai martaba sarkin Kano Alhaji Muhammadu Sanusi na II ya kawo game da son kafa dokar da za ta hana duk wani wanda ba zai iya rike mace ba yin aure da kuma hana yadda ake ta samun yawaitar sakin aure haka kuma da yadda ya kamata a ce malamai sun taka muhimmiyar rawa wajen rage hakan.

  To sai dai tambaya a nan ita ce shin idan har wannan doka mu kaddara jihohin arewacin Nijeriya da ke mafiya rinjaye musulmi ne ,su kuma musulmi tsiraru marasa rinjaye da ke zaune a Kurmi da sauran sassan inda ba su da rinjaye yaya dokar za ta rika yin tasiri gare su kuma su Musulmi mazauna Kudanci wane mataki Limamai da malaman su za su dauka .Duk da ma wasu karin bayanai Sheikh Kabiru Yakubu Sa\’ad  babban limamin barakin soja birged ta 13 ta Sojan Nijeriya da ke Kalaba,  kuma shugaban kungiyar limaman da suka hada da daukacin na  jihar Kuros Riba ya yi bayani mai  gamsarwa cikin tattaunawarsu da wakilinmu na Kudanci MUSA M.KUTAMA. Ga yadda tattaunawar tasu ta kasance:-

  GTK:Allah gafarta malam mai martaba sarkin Kano Alhaji Muhammadu Sanusi ya kawo shawarar a kafa doka da za ta hana duk wani wanda ya san ba zai iya rike mace ba kara aure da kuma hana yadda sakin aure ke yawaita, mene ne za ka ce kan haka?

  Sheik Kabiru Yakubu   Saad: Auzubillahi mina samiul alim a\’uzubillahi minashshaidanir rajim Bismillahirrahmanir Rahim. Ah! Wannan tambaya da ka yi min kan wannan lamari ina ga ya yi daidai shi daman musulunci bai bar mu haka ba ba tare da ya yi mana bayani ba .To shi mai martaba sarkin Kano da ya kawo wannan shawara yake kokarin dabbaka wannan  doka shi ne Musulunci yana son ya dawo wa da mutane hankalin su kan akwai wanda mabukaci ne akwai kuma wani wanda shi ba ya da bukatar auren ma akwai kuma wanda yake auren farilla ne gare shi wani mustahabi ne ,to amma gaskiya ne yanzu yadda ake yanayin auren yanzu sai ka ga abubuwan ne sun wuce gona da  iri wadan su ma auren sunayi don wasa ne ai wane yana da mata 2 ko 3 ni ma bari in kara za ka ga wasu ba su da wata kwakkwarar sana\’a a wata ma ba zai iya kawo naira dubu 5 ba a gidan nasa amma ya tara iyalai ,ya tara mata babu adalci kullum fada shi ya sa ga shi za ka ga yaran an haifa an kasa tarbiyar tar da su ga barace-barace ,abubuwa dai na barna daban-daban to mutum ne ya tara iyali ya kasa ciyar da su ya kasa tarbiyartar dasu me kake tsammani?. Sai fa barna da sace-sace da sauran su.

  GTK:Sheik Kabiru kana ganin kafa dokar zai iya magance wadan can matsaloli?

  Sheik Kabiru Yakubu Sa\’ad:  Sosai !  insha Allahu zai magance tun da an saki abun ne ba wata doka idan ka yi aka tabbatar da cewa karfinka bai kai ba ka yi, to sai a hukuntaka a kai ka kotu a hukuntaka a nuna ma abin nan da ka yi ka yi kuskure ai ka ga a cikin maganarsa ya ce wadanda ba su da iko, bas u da hali da za su auri fiye da mata daya amma idan kana da hali bai ce ya hana ma aure ba idan kana da hali ka rike fiye da 1. falillahil hamdu wanna babu damuwa to yin dokar gaskiya zai rage abubuwa da dama kwarai da gaske .

  GTK: Akramakallahu baka ganin cewa za,a iya fuskantar tirjiya waje aiwatar da dokar ko masu aiwatar da ita ko kuma wadanda za a aiwatar a kan su a nan wace irin shawara za ka bayar  ?

  Sheik Kabiru  Yakubu Sa\’ad: To kasan dama mutane haka ne idan abu ya bullo dole sai ka samu wadanda suke goyon baya da kuma wadanda ba sa goyon baya amma idan aka duba aka bi abun a hankali aka cire son zuciya za ka ga cewa akwai amfani maimakon \’ya\’yanmu mata da suke ta aure wata 1.  ko 2 sai ka ji an saki yarinya mene ne dalili sai ka ji ainihin babu ci babu sha,  to ai ma ka ga wulakanci ne  mace ta tafi gidan aure ana mata fatar ya dore har mutuwa amma wata daya biyu ta fito tana gida an bar ma ita ta riga ta zama takumbo [bazawara] gara ta natsu tana gidan ta samu wanda zai aure ta ya fi a ce a yi auren a zo a fita shi ya sa ga zawarawan nan babu iyaka idan ka tambayi dalilin sai sai ka ji wani ma ba wani abun da ya taka kara ya karya ba ne rashin iya ciyar da gidan ne idan aka kafa dokar insha Allahu za a ji dadi.

  GTK: Yaya kake ganin idan an yi nasara majalisar dokokin Kano ta amince ya zama doka sauran jihohin arewacin Nijeriya da musulmi ke da rinjaye kana ganin su ma za su dau hannu abin ai iya yin tasiri?.

  Sheik Kabiru Yakubu Sa\’ad: To aid a yake ba wata sabuwar doka ba ce dama dai cikin Alkur\’ani ne da Sunnar Manzo s.a.w. kuma idan mutum Musulmi ne yana imani da Allah da ManzonSa s.a.w. ya kamata shi ba ma sai an gaya masa cewa ya bi wannan abin kawai dai kawai gyara kansa zai yi ya bi wannan doka saboda ana tunatar da shi abun da ya manta ne .

  GTK:To wani abu da zai dan so ka yi mana karin bayani misali idan mu kaddara jihohin arewa sun kafa irin wannan  doka Musulmi kuma fa da ke sauran sassan  na Kurmi da ba su da rinjaye kuma fa ya kake ganin dokar za ta yi tasiri a irin wadannan wurare?

  Sheik Kabiru Yakubu Sa\’ad :To Musulmi-musulmi ne shi ya sa muke da malamai da limamai muna yin wa\’azi kuma kuna zuwa kuna sauraren mu shi ya sa ba mu taba kawo wani abu ba da ya fita daga cikin aya ta Kur\’ani ba ko Hadisin Manzo ba ko ijma,in malamai ba duk abunda ake yi muswuluncin akeyi don haka suma musulmin kudu musulmai ne duk da yake sun samu kansu kara zube ba tsawatarwa  ba fadakarwa  amma idan ka duba ai ya shafi har nan din shi ya sa yara a nan idan ka duba musulmai ne ba tarbiyya iyayensu sun haifesu ba su ma san cin su ba balle shan su ba su san kwanan su ba  ba daukar dawainiyar su  ga shi ai ka ji wani yaro an kashe shi sai da ya yi kwanaki sannan ubansa ya samu labari ku san sati biyu ma ko kwana goma da kashe yaron ga shi ana ta kawo mana korafi yaran musulmin  iyayen iyalai sun yi masu yawa ga shi abin da ake samu ba yawa ba\’a kula da gidan an bar su sun lalace, don haka tun da mu ne a Kudu Allah ya  dora wa  shugabancin wannan insha Allahu za mu sa ido kuma zamu ci gaba da fadakarwa muna tunatar vda mutane abinda ya kamata suyi na hakkiin iyalan su da na \’ya\’yan su shekaranjiya ina layin Bagobiri wani ya yi aure mun yi masa fada sosai kan irin wannan, na nuna masa matsalolin mu ,mutum ya yi aure ya gagara ciyarwa saki da sauran su  bah aka ake yi ba Musulunci ya riga ya tsara wannan da yadda za ka yi hatta shi saki da mai martaba yake magana a Musulunci baka sakin matarka haka kawai daga abu ya hada ku  ka ce ka saki ba a haka yadda ka nemi auren da shaidu haka ma Musulunci ya nuna wajen sakin sai ka kawo shaidu ka fadi mene ne  dalilinka tun da  Allah Madaukakin sarki ya ce a yi sulhu idan sulhun ba zai yi ba a kai ga iyaye idan aka kai gare su abun bai yi ba, to shi kenan sai a kai ga sulhu na tsari an addinmin Musulunci .

  GTK: Akramakallahu idan mun fahimceka kamar kungiyar ku ta liimamai da malamai ma za ta rika sa ido ita ma ta rika aiwatar da wannan doka musamman yadda a nan Kurmi ake yi wa aure da saki karan tsaye?

  Sheik  KabiruYakubu Sa\’ad : Wannan abu ne mai sauki da yake dukkan limaman da malaman muna tare , tare ake komai kuma insha Allahu to za mu sa ido mu gani duk inda za a yi aure ko akwai saki mu tabbatar mun bi mun ga dokar da a kan sakin idan sakin ba a kan daidai ba ne mu tsawatar  mu sa a mayar idan kuma abun da ya kamata a yi saki ne to shi kenan sai mu bi yadda ya kamata a yi sakin .

  GTK: Kamar yaushe za ku fara sa idon ?.

  Sheik Kabiru Yakubu Sa\’ad:  Ai wannan ba matsala ba ce mu dama muna da masu sa idon kan irin wadannan a bubuwan  tun daga lokacin da muka kafa wanna kungiya babu wata magana irin wannan ta saki barkatai kasan duk wata magana irin wannan  a matsayina idan ta zo ba zan bita da sauki ba sai na tsaya na tabbatar meye dalili meye faruwa idan wanda za a yi sulhu ne a sulhunta idan wanda ya gagara ne musan waye hakkin sa haka ya  kamata ayi insha Allahu .Daga yanzu in Allah ya yarda za mu ci gaba da sa  ido.

   

   

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here