\’Bai Kamata Barazana Ta Hana Buhari Ziyara Ba\’

0
890

Rabo  Haladu Daga Kaduna

ANA samun ce-ce-ku-ce a baya-bayan nan tsakanin \’yan al\’ ummar kasar nan  kan ziyarce-ziyarcen da muƙaddashin shugaban ƙasa, Farfesa Osinbajo ke kai wa wasu sassa.
Masu sharhi na ganin ziyarar da ƙarin wasu matakai sun taimaka gaya wajen samun kyautatuwar harkokin tattalin arziƙi da zamantakewar al\’umma, baya ga inganta alaka tsakanin gwamnati da jama\’ar da ake mulka.
Wani mai sharhi kan harkoki a Nijeriya, Ja\’afar Ja\’afar na ganin, ziyarar ta taimaka wajen bunkasa yawan man fetur ɗin da Nijeriya ke hakƙowa a yankin Naija Delta, wanda a baya ya yi fama da ayyukan matasa tsageru masu fasa bututan mai da iskar gas.
A ƙarshen watan Fabrairu ma, Osinbajo ya kai ziyarar ba-za ta ɗaya daga cikin filayen jiragen saman ƙasar da ke Lagos, har ya kewaya wasu sassa don ganin halin da suke ciki.
Ya kuma kai irin wannan ziyara zuwa kudancin jihar Kaduna mai fama da hare-haren da ake alaƙkanta su da ƙabilanci, har ma ya bai wa mutanen da abin ya ritsa da su tabbacin ɗaukar matakai don kawo ƙkarshen rikicin.
A baya, wasu masu sharihi sun sha sukar shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari a kan rashin ziyartar sassan ƙasar don ganin halin da al\’umma ke ciki.
An yi wa shugaba Muhammadu Buhari addu\’o\’in samun lafiya a coci-coci da masallatai da ke fadin kasar nan.
Ja\’afar Ja\’afar ya ce \”karo biyu shugaba Muhammadu Buhari yana shirya kai ziyara zuwa yankin Naija Delta, amma sai ya fasa sakamakon barazana daga tsagerun matasan yankin\”.
A cewarsa kamata ya yi shugaban ya yi amfani da dabarun mulki wajen shawo kan tsagerun ta yadda za su riƙa yi masa maraba maimakon kashedin kada ya kai ziyara.
Masharhancin ya ce wasu makusantan shugaba Buhari ba za su ji daɗin irin wannan ziyara da muƙaddashin shugaban yake kai wa ba, don kuwa a cewarsa ziyarar na fito da gazawar Buhari ne ƙarara.
Ya ce magoya bayan Muhammadu Buhari za su so a ce shugaban ne yake kai wannan ziyara da kansa, maimakon muƙaddashinsa abin da a siyasance ke ƙara fito da ƙimar Osinbajo.
Fadar shugaban kasa dai ta yi watsi da irin waɗannan raɗe-raɗi da ake yaɗawa inda ta ce muƙkaddashin shugaban ƙkasar ba ya yin wani abu sai ya tuntuɓi shugaba Muhammadu Buhari.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here