YADDA AWOLOWO YA HANA KASAR NAJERIYA WARGAJEWA – inji Gawon

0
869

Daga Unman Nasidi

TSOHON shugaban kasa Janar Yakubu Gowon ya bayyana yadda marigayi Obafemi Awolowo ya hana Najeriya wargajewa a lokacin yakin basasa na Biyafara. Gowon ya bayyana haka ne a ranar tunawa da marigayi Awolowo.
Yakubu Gowon ya ce a lokacin Cif Obafemi Awolowo yana Minista, Najeriya ba ta karbi aron kudin ko sisi ba har aka kammala wannan yaki na basasa. Gowon ya ce marigayi Awolowo da sauran wadanda ke gwamnati suka ba sa shawarar yadda za a tafiyar da gwamnati.
A taron dai Gawon ya ce bai taba furta cewa kasar Najeriya tana da kudi har ta rasa abin da za ta yi da su ba a lokacin yana shugabanci. An dai dade ana yawo da wannan maganar da sunan tsohon shugaba Yakubu Gowon din.
Gowon ya ce idan da su Awolowo za su tashi daga kabari ba za su ji dadin ganin yadda Najeriya ta zama ba. Kwanan nan shugaba Buhari ya kira Yakubu Gowon din inda ya yi masa ta’aziyar rasuwar kanwarsa Martha Kande Audu wadda ta cika kwanakin baya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here