Yaki Da Cinhanci: Kotu Ta Daure Tsohon Gwamna Shekara Biyar A Yola

0
764

Muhammad Saleh, Daga Yola

WATA babbar kotu a Yola, ta daure tsohon gwamnan jihar Adamawa Barista Bala James Nggilari, shekaru biyar a gidan kasu, biyo-bayan rashin bin ka’idojin doka a lokacin yake shugabantar jihar a matsayin gwamna mai cikakken iko.

Da yake yanke hukuncin babban alkalin alkalan jihar Mai shariya Natahan Musa ya ce kotu ta samu tsohon gwamnan da laifin bada kwangilar sayo motoci 25 ba tare da bin ka’idar da doka ta tanadar ba, don haka kotu ta daureshi shekaru biyar ba tare da daukaka kara ba.

Dama dai hukumar yaki da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC ta kalubalanci tsohon gwamnan a kotu da wasu manyan mukarrabansa biyu Andrew Welye da Sunday Lamurde, sakataren gwamnatin da kuma kwamishinan kudi.

Hukuncin kotun dai ya kuma wanke sakataren gwamnatin Andrew Wwlye da kwamishinan kudin Sunday Lamurde, bisa rashin gamsasshiyar hujjar tukumar da hukumar EFCC ke mu su.

 Mai shari’a Nathan Musa, ya ce tsohon gwamna Nggilari ya’yi fatali da tsarin dokokin da jihar ta tanada ya’yin bada kwangilar sayo motoci 25 ga kwamishinoni akan kudi naira miliyar 167 da dubu dari takwas ba tare la’akari da ka’idar dokar ba.

 Lauya da ke tsayawa tsohon gwamnan Mista Samuel Toni (SAN), ya nemi afuwa da cewa “Nggilari ya bada muhimmiyar gudumuwa lokacin da yake gwamna a jihar, yataimaka a fannin dakushe ‘yan bindiga”.

Alkalin kotun dai ya ce tsohon gwamna Nggilari yana da zaben kan gidan kasun da yake bukatar zama a fadin kasar nan, “amma yanzu zaka zauna a gidan yarin Yola”.

Ya yabbana hukuncin da ya yanke na tura tsohon gwamnan gidan kasu a matsayin ko zai zama darasi da gwamnonin da suke kujeran mulki a halin da ake aciki.

“ina fata wannan hukunci zai zama darasi ga sauran gwamnoni da suke kan kujeran mulki” injishi.

Da yake magana da manema labarai kafin tafiya da shi gidan yari tsohon gwamna Bala Nggilari, ya ce zai daukaka kara a kan hukuncin da kotun ta yanke mishi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here