Za A Iya Samun Gidan Yankan Kai A Kano — Ganduje

0
951

Rabo Haladu Daga Kaduna

GWAMNA Ganduje ya ce watakila za a iya samun gidajen yankan kai a birnin Kano
Gwamnan jihar Kano  Abdullahi Umar Ganduje, ya ce birnin Kano na fama da matsalar satar kananan yara.
Satar yara kanana dai ta yi kamari a birnin na Kano a \’yan watannin da suka gabata musamman a wasu sassan gabashin birnin.
Hakan ne kuma ya sanya sanya mazauna yankunan gudanar da zanga-zanga domin jan hankalin gwamnati ta dauki matakin shawo kan matsalar.
To sai dai gwamna Ganduje ya ce yanzu haka suna kokarin shan kan matsalar nan ba da jimawa ba.
Ya kuma amsa tambaya kan shin ko akwai gidan yankan kai a Kano?
Ya ce bacewar yaran kamar yana da nasaba da haka domin  inba gidan yankankai maizai sa kullun yara bacewa.
Amma za mu bincika domin gano gaskiyar lamarin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here