MUSA MUHD KUTAMA, Daga Kalaba
GOBE Asabar idan Allah ya kai mu Jami’ar Kalaba za ta karrama mai alfarma Sarkin Musulmi Sa’adu Abubakar na III da digirin girmamawa tare da shahararren dan siyasar jihar sakkwato Alhaji Umarun Kwabo A.A.Jarman Sakkwato .Haka kuma daga cikin dalibai da za ta yi bikin yayewa su kimanin dubu 13, da 347 ake sa rai a fage daban-daban na ilmi za a yaye.
Da yake ganawa da manema labarai ranar Alhamis a ofishinsa mataimakin shugaban jami’ar Farfesa Zana Akpagu ya ce baya ga bikin yaye daliban akwai wasu muhimman ayyuka da Jami’ar za ta kaddamar da suka hada da gina tsangayar karatun hada magunguna da na koyon injiniya, sauran su ne na koyon aikin jarida da kuma samar da karin wasu kwasa-kwasai .
Sai dai mataimakin shugaban Jami’ar ya yi bayanin cewa matsalar karancin kudi ce ta fi addabar Jami’ar karshe ya bayar da bayanin nau’o’in digiri da za a raba wa dalibai da suka yi nasara kamar haka:-
Babban digiri mutum 1,437 mai biye masa kuma mutane dubu 11 da 910 sannan rukunin ‘yan babu yabo ba fallasa 2,900. Ya koka da matsalar halayen wasu dalibai da suke kin biyan kudin makaranta wanda a cewarsa idan da suna biya a kan kari da makarantar ta samu kudaden da za ta aiwatar da ayyukan raya makarantar, inji shi.