WANI gagarumin fada ya barke a kasuwar sabon Panteka dake hanyar babban titin Nnamdi Azikiwe lokacin da wani mutumi dan kabilar Igbo ya sanya ma karensa suna Muhammad.
Jami’an hukumar sojin Najeriya da suka mamaye yankin don dawo da zaman lafiya da doka bayan barkewar fadan sun rufe kasuwar.
Kasuwar Panteka ta kasance matatarar masu gyaran ababen hawa a jihar, wanda ke dauke da garejin bakanikai da yawa.
Wani shaidan gani da ido Aminu Ibrahin ya ce rikicin ya fara ne lokacin da wani Muhammad ya siya kare sannan ya sanya ma karen sunan wani mutumin Igbo mai siye da siyarwa.
“Tun da yaron ya sanya ma karen sunan dan kasuwar, dan kasuwar na ta gargadin shi lokuta da dama kan cewa ya canja wa karen suna, amma mammalakin karen Muhammad ya ki.
Wannan ya sa shi ma Ibere ya siya kare sannan ya sanya masa suna Muhammad, a lokacin ne rikicin ya barke sosai,” cewar shaidan na gani da ido.
Ya ce sai fada ya daure tsakanin \’yan kasuwa Hausawa da Inyamurai a kasuwar wanda ya kai har saida \’yan sanda suka rufe kasuwar.
Ba a samu daman jin bayani daga bakin kakakin yan sanda ba a lokacin da ake kawo wannan rahoton kamar yadda bai amsa kiran wayarsa ba.
WANI SABON RIKICI YA AUKU A KASUWAR FANTEKA KADUNA
Daga Usman Nasidi