Fulani Na Alfahari Da Matakan Gwamna El-Rufa\’i

0
1065

Jabiru A Hassan, Daga Kano.

ARDON gundumar Haskiya da ke yankin karamar hukumar Kubau Alhaji Wakili Manya  ya  nuna gamsuwar sa bisa yadda gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El~Rufa\’i  yake daukar matakai na  magance satar shanu da garkuwa da mutane a fadin jihar.
Ya yi wannan tsokaci ne a zantawar su da wakilin mu  karshen wani taro da ya yi da fulani makiyaya a Falgore cikin yankin karamar hukumar Doguwa, inda ya nunar da cewa gwamnatin jihar kaduna bisa jagorancin Gwamna Nasir  El~Rufa\’i  tana kokari matuka wajen inganta zaman lafiya da kwanciyar hankali  tsakanin fulani makiyaya da manoma wanda hakan ta sanya al\’amura suka fara daidaita a jihar.
Sannan ya yi kira ga  fulani makiyaya da su taimakawa kokarin gwamnati na inganta zaman lafiya da kwanciyar hankali a Jihar Kaduna dama kasa baki daya, inda kuma ya bukaci  masu rike da makamai  masu barazana ga zaman lafiya da su  ci gaba da mika su ga hukumomin tsaro ta yadda shirin bunkasa zaman lafiya zai cimma nasara.
Ardo Wakili  Manya ya kuma yi amfani da wannan dama wajen yin kira ga gwamnatin Jihar Kano da ta kara daukar matakai na dakile aiyukan masu satar mutane da dabbobi  musamman a yankunan kananan hukumomin da suka yi iyaka da dajin Falgore domin a hadu a kawar da duk wata barazana data jibinci satar mutane da dabbobi a jihohin biyu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here