Isah Ahmed, Jos
ALHAJI Dogara Isiyaka da ke zaune a garin Jos babban birnin jihar
Filato, wani tsohon ma\’aikacin gandun daji ne da ya yi shekaru 55 yana
aikin gandun daji, tun a lokacin mulkin turawa.
A wannan tattaunawa da ya yi da wakilinmu, ya bayyana cewa a duk
duniya babu kasar da ta kai yankin arewacin Nijeriya kasar noma. Ya ce
amma ana lalata wannan kasar noma a yankin saboda sare itatuwan da
ake yi a kullum.
Ga yadda tattaunawar ta kasance
GTK; Da farko zamu so muji tarihin rayuwarka
Dogara Isiyaka; Ni dai sunana Alhaji Dogara Isiyaka kuma ni mutumin
garin Keffi ne dake jihar Nasarawa. Amma a yau ina da shekara 78 da
zama a nan garin Jos. Kuma a yanzu ina da shekara 127 da watanni 6, a
duniya.
Nayi makarantar elementari kuma nayi aikin gwamnati tun a zamanin
turawa a sashin shuke shuken itatuwa, har na tsawon shekara 55.
Daga nan nace zan je na huta. Don haka nayi ritaya har ya zuwa wannan
lokaci da muke ciki. A yanzu Ina karvar fansho guda biyu daya a
gwamnatin tarayya, daya kuma a gwamnatin jihar Filato.
GTK; To, yaya zaka kwatanta mana yadda ake kula da gandun daji
ada da kuma wannan lokaci da muke ciki?
Isiyaka Dogara; Wannan tambaya tana da mahimmanci domin maganar aikin
kula da gandun daji a Nijeriya, yanzu komai ya lalace. Kuma abin da
ya kawo haka shi ne son zuciya da kuma rashin sani. Domin idan aka
bari itatuwa suka qare a kasar nan, za a shiga wata masifa wadda sai
dai Allah ya kiyaye.
Domin idan hamada ta mamaye arewacin kasar nan babu wani abu da zamu
iya yi. Kuma itace yana daya daga cikin abin da yake hana hamada
mamayar kasar nan.
A duk duniya babu kasar da ta kai yankin arewacin Nijeriya kasar
noma. Amma ana son abar wannan kasar noma ta lalace gabaki daya,
sakamakon kwararowar hamada saboda sare itatuwan da muke yi a Kullum.
Ada duk gandun dajin da muke da su a kasar nan, babu wani mutum da ya
isa yaje ya sari itace ko kuma ya yanki ciyawa a ciki. Amma a yanzu
abin ba haka yake ba, yanzu ma babu gandun dajin domin ana sare
itatuwa ta ko\’ina a kasar nan.
Ada kowanne wuri zaka ga anje an shuka itatuwa don kasa ta zamo
dausayi mai kyau. Idan akwai itatuwa a gona, misali wani yana da
gona mai fadin eka 200 amma babu itace a
ciki. Wani kuma yana da gona
mai fadin eka 100, amma yana da itatuwa a ciki, to amfanin gonar da
zai samu sai ya ninka yawan wanda yake da gona mai fadin eka 200
babu itatuwa a ciki.
Ada itatuwa suna da dokoki masu karfi, domin idan an ce wannan gandun
daji ne ba a taba komai a ciki. Ko futsari mutum ya yi a ciki za a
iya kama shi. Kuma ada akwai wadannan gandun daji a ko\’ina a kasar
nan. Domin itatuwa sune lafiyar dan adam da dabbobi. Domin iskar da
itace yake kawowa yana taimakon dan adam da dabbobi.
Amma yanzu ana ta sare itatuwa a Nijeriya kuma ba a dasa wasu. Idan
muka cigaba da yin haka za a wayi gari babu itatuwa a Nijeriya.
GTK;; To mene ne mafita kan wannan al\’amari?
Dogara Isiyaka; Mafita ita ce a koma an sake kafa gandun dazuzzuka a
kasar nan. A dauki ma\’aikata masu ilmi wadanda za su tafiyar da wannan
aiki. Idan ba a yi haka ba, nan gaba ko itacen girki ba za a samu ba a
Nijeriya.
Saboda haka gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihohin kasar nan su
koma kan harkokin inganta itatuwa. Domin a raya kasar nan, a sami wajen
noma. Itatuwa suna da matukar amfani kan aikin gona. Ko a gida itace
yana da matukar amfani kwarai da gaske. Domin idan babu itace a gida,
iska za ta iya kwashe rufin gidan amma idan da itace a gidan itacen zai
iya tare iskar.
GTK;; Wanne irin tasiri ne kake ganin kasar nan zata samu idan aka
rungumi harkokin itatuwa?
Isiyaka Dogara; Babu shakka idan muka rungumi harkokin itatuwa a kasar
nan, za mu sami babban amfani. Domin itatuwa suna da matukar
mahimmanci a ko\’ina a duniya ba a Nijeriya kadai ba. Saboda haka idan
kaje kasashen turawa zaka ga kowanne babban gari yana cike da itatuwa.
Domin itatuwa suna bai wa mutane lafiya kuma suna tsare wasu abubuwa
a gidajen mutane. Saboda haka idan aka dawo da maganar shuka itatuwa
a Nijeriya za a sami babban ci gaba.