Jabiru A Hassan, Daga Kano.
AN bayyana cewa Nijeriya za ta ci gaba da samun ci gaba ta fuskar tattalin arziki da zaman lafiya saboda kyawawan manufofin gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Wannan tsokaci ya fito ne daga Alhaji Usman Dan Gwari, wani fitaccen mai sana\’ar kayan Gwari dake kano, inda ya nunar da cewa yadda ake tafiya a halin yanzu ya isa a fahimci cewa kasarnan tana samun ci gaba ta fannin aikin gona da kuma cinikayya wadanda sune kashin bayan ci gaban kowace kasa, sannan ya bada misalai masu yawa kan yadda kayan amfanin gona suke daraja sakamakon albarkar da Ubangiji y asanya masu.
Alhaji Usman Dan Gwari ya kuma bayyaba cewa sana\’ar gwari ta zamo abar alfahari wajen bude hanyoyi na dogaro da kai sannan tana bada kashi 70 na guraben aiyukan yi a kasa, don haka zasu ci gaba da bunkasa wannan sana\’a ta yadda nan gaba kadan zata kawar da talauci a kasa da kuma bunkasa hanyoyi na dogaro da kai.
Daga karshe, yayi fatan alheri ga shugaba Muhammadu Buhari saboda dawowa gida da yayi daga hutun neman magani da yaje kasar ingila, tareda yabawa \’yan Nijeriya bisa addu\’oi da suka yi tayi masa na samun cikakkiyar lafiya.