Yadda Aka Gudanar Da Murnar Dawowar Shugaban Kasa Buhari A Garin Jos

0
1033
Isah Ahmed, Jos
DUBBAN al\’ummar da suke zaune a garin Jos babban birnin jihar Filato,
da suka hada  maza da mata ne suka fito suka gudanar da gangamin
murnar dawowar shugaban kasa Muhammad Buhari a ranar juma\’ar da ta
gabata.
Wakilinmu ya ganewa idonsa yadda dubban mutanen suka mamaye hanyoyin
cikin garin wasu kan motoci wasu a kafa suna ta murnar dawowar
shugaban kasa.  Hanyoyin cikin garin kamar na Bauchi road da unguwar
rogo da Nasarawa da Rikkos da Zariya road duk inda mutum ya zagaya a
wadannan hanyoyi, zai ga yadda mutane suka fito suna ta murna da
godiya ga Allah kan dawowar ta shugaban kasa Muhammad Buhari.
A zantawarsa da wakilinmu kan dawowar ta shugaban kasa, Ko\’odinaten
kungiyar Jama\’atu Nasril Islam na shiyar arewa ta tsakiya Sheikh
Abdul\’azeez  Yusuf ya bayyana cewa mun yi godiya ga Allah kan alherin
da ya yi mana na dawowar shugaban kasa Muhammad Buhari cikin koshin
lafiya.
Ya ce shugaban kasa mutum ne wanda kowa ya gamsu da yadda yake gudanar
da mulkin sa a Nijeriya.
\’\’Addu\’o\’in da \’yan Nijeriya suka yi na Allah ya ba shugaban kasa
lafiya, ya nuna cewa al\’ummar Nijeriya suna da kyakyawan zaton alheri
da za a samu a mulkinsa. Shi shugabanci idan mutum ya fara da tsoran
Allah, ya yarda cewa Allah ne ya bashi shugabancin to Allah zai tsare
shi\’\’.
Ya yi kira ga  al\’ummar Nijeriya su cigaba da yiwa shugaban kasa
addu\’a  kuma su  cigaba da goya masa baya kan ayyukan alherin da ya
faro. Kuma kowa ya bada gudunmawarsa a wajen harkokin tafiyar da kasar
nan  ta hanyar adalci da tsoron Allah.
Daga nan ya yi kira ga shugaban kasar ya kara godiya ga Allah kuma ya
tsaya kan kyakyawar niyarsa ta tafiyar da al\’ummar kasar nan kan
adalci. Sannan kuma ya rungumi mataimaka da suke taimaka masa a kan
gaskiya.
Shi ma a zantawarsa da wakilinmu shugaban kungiyar dillalan mota ta
kasa reshen jihar Filato kuma shugaban kamfanin sayar da motoci na
Kega Motors Alhaji Yahaya Muhammad Kega  ya bayyana cewa mun yiwa
Allah godiya kan wannan baiwa da ya yi mana na dawowar shugaban kasa
Muhammad Buhari.
Ya ce dama mutane ne suke nuna jahilci, sun manta cewa  duk rayuwar
\’yan adam tana hanun Allah ne.
\’\’Wannan abu da ya faru ga shugaban kasa, Allah ya nuna cewa shi ne
yake da komai kuma shi ne yake da kowa. Saboda haka muna fatar dawowar
shugaban kasa zata zama babbar alheri ga al\’ummar Nijeriya\’\’.
Ya ce Allah ya daure mutanen Nijeriya, ya baiwa shugaban kasa Buhari,
domin duk abin da s zai yi a Nijeriya da wuya a sami wanda zai ku shi
shi, idan ba \’yan adawa ba.
Ya yi kira ga \’yan Nijeriya su fahimci cewa ba a taba samun gwamnati
take da alkibla kamar wannan gwamnati ta Buhari ba.
Ya ce sai ranar da ba Buhari,  sannan \’yan Nijeriya zasu dada
fahimtar abubuwan alherinsa. Don haka ya kamata a bashi hadin kai
domin ya sami aiwatar da wadannan abubuwa.
A zantawarsa da wakilinmu kan dawowar ta shugaban kasa, shugaban
kungiyar Katsinawa da Daurawa mazauna jihar Filato Alhaji Ibrahim
Abubakar ya yi kira ga Shugaban kasa Muhammad Buhari ya yiwa Allah
godiya kan yadda ya bashi arzikin al\’ummar Nijeriya.
Ya ce  irin adalcinsa ne yasa mutanen Nijeriya suke son sa suke
kaunars, don haka ya yi  kira ga shugaban kasar ya cigaba da wannan
adalci da yake nunawa al\’ummar Nijeriya.
Daga nan ya yi kira ga al\’ummar Nijeriya a cigaba da yiwa shugaban
kasa addu\’a Allah ya bashi ikon aiwatar da abubuwan alherin da ya
sanya a gaba.
Shima a zantawarsa da wakilimu shugaban kungiyar masu Keke Napep na
karamar hukumar Jos ta Arewa, Malam Dahiru Hassan cewa ya yi wannan
rana da Allah ya dawo mana da shugaban kasa, wata rana ce da ya kamata
duk wani dan Nijeriya ya yiwa Allah godiya.
Ya  roki Allah ya baiwa shugaban kasa  damar aiwatar da abubuwan
alherin da ya sanya a gaba a Nijeriya. Ya yi kira ga shugaban kasa ya
ci gaba da rike kowa da kowa a Nijeriya.
A zantawarsa da wakilinmu  mai baiwa gwamnan jihar Filato shawara na
musamman kan harkokin mulki kuma ko\’odinatan ayyuka na kasa na
kungiyar kwankwasiya Alhaji Nuradeen Inuwa Maigado  cewa hakika
dawowar shugaban kasar wani babban abin farin ciki ne ga al\’ummar
Nijeriya. Musamman ganin cewa an  taru a ko\’ina a kasar nan, an yi
ta yi masa  addu\’ar Allah ya bashi lafiya kuma Allah a cikin ikonsa ya
karbi addu\’ar ya ba shi lafiya yanzu ga shi har ya dawo gida Nijeriya.
Ya yi  kira ga shugaban kasa ya dubi irin soyayyar da \’yan Nijeriya
suka nuna masa saboda halayensa na kwarai, ya cigaba da nuna irin
wadannan halaye.
Ya yi  kira ga \’yan Nijeriya  su gyara halayensu domin shugaban kasa
yana iyakar kokarinsa wajen ganin ya kawo sauki ga rayuwar al\’ummar
Nijeriya. Amma wasu \’yan Nijeriya suna dakile wannan kokari da yake
yi.
 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here