Mutum 35 Sun Mutu Wasu 25 Sun Jikkata A Hadarin Mota A Yola

0
855
Muhammad Saleh, Daga Yola

RUNDUNAR ‘yan sandan jihar Adamawa, ta tabbatar da mutuwar mutane 35 da jikkata wasu mutanen 25 a wani hadarin mota a kan hanyar Yola-Ngurore ranar lahdin da daddare.

SP Othman Abubakar shi ne kakakin rundunar ‘yan sandan ya ce lamarin ya faru ne misalin karfe bakwai da yamman ranar Lahadi, sakamakon gudu da ludi fiye da kima da direbar motar Tirelar ya’yi.

Ya ce yanzu haka rundunar da kaiga tantance mutane 35 da suka mutu, da wasu 25 da su ka samu munanan raunuka, SP Othman ya gargadi jama’a da su guji ludi fiye da kima da yawan gudu, da cewa ita ce hanyar kubutar da kai daga hadura.

Bayanai sun tabbatar da cewa motar ta fito ne daga garin Song, dauki da shanu 60 da kuma mutane sama da 100 mafiyawa matasa, da dama sun tafi kasuwar maici ranar Lahdi ne, domin gudanar da aikin karfi.

Ganau dai sun tabbatar da cewa adadin mutanen da suka mutu ya fiye hakan, domin kuwa har yanzu lokacin hada wannan rahoton wasu mutanen ba’agansu ba, majiyar ta ce wasu ‘yan uwan mamatan sun dauke gawarwakin ‘yan uwansu da hadarin ya rutsa da shi.

Wata majiyar ta ce baya ga mutanen da suka mutu a yayin hadarin, akwai kuma shanu kimanin 13 da su ma suka mutu sakamakon hadarin.

Jama’ar garin Ngurore dake karamar hukumar Yola ta kudu, suna ci gaba da juyayin mummunar hadarin da irinsa bai taba aukuwa a garin ba.   

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here