Daga Usman Nasidi
WATA dalibar makaranta mai suna, Raliya Suleiman, ta rasa idonta na dama bayan daya daga cikin malamanta ya doke ta da bulala a kan ido.
Raliya ta kasance dalibar makarantar karamar sakandare na gwamnati dake Kachai, an rahoto cewa wani malami a makarantar, Moses Aura ne ya zane ta saboda tayi lattin zuwa makaranta a ranar Alhamis, 23 ga watan Fabrairu, 2017.
Rahotanni sun bsyyana cewa sakamakon dukar da malamin yayi mata, bulala ya sami dalibar a idon ta na dama, wannan ne yayi ma idon lahani na din-din-din. A halin da ake ciki, kawun Raliya, Sani Abubakar ya tabbatar da al’amarin.
Ya ce: “A wannan ranar, 23 ga watan Fabrairu, 2017 Raliya tayi lattin zuwa makaranta sai malamin, Moses Aura ya bukaci ita da sauran dalibai da su tsuguna su jira shi.
Lokacin da ya dawo, sai ya fara dukan ta sannan bulalan ya same ta a idon ta na dama. A take aka garzaya da ita zuwa asibitin ido, Kaduna, amma abun bakin ciki, sun ce ruwan idon ya tsiyaye kuma babu abunda zasu iya yi don dawo da idon.”