Duk Mai Tunani Ba Zai Yi Wa Buhari Mummunan Fata Ba-Archibishop Kaigama

    0
    891

    Isah  Ahmed, Jos

    ARCHIBISHOP  Ignatius Kaigama  shi ne Archibishop na darikar katolika na Jos kuma shugaban bishop bishop na darikar katolika a Nijeriya. A wannan tattaunawa da ya yi da wakilinmu kan dawowar shugaban kasa
    Muhammad Buhari, daga jinyar rashin lafiyar da ya tafi zuwa kasar Ingila. Ya bayyana cewa duk mai tunani ba zai yi wa  shugaban kasa Muhammad Buhari mummunan fata ba. Don haka ya yi kira ga masu yi wa Buhari mummunan fata  su sake tunani, su dawo su ci gaba da yi masa addu\’a. Domin Allah ne ya kawo shi don ya ceto Nijeriya.
    Har\’ila yau ya yi kira ga shugaba Buhari  ya rika tantance  irin shawarwarin da wadanda suke kusa da shi suke ba shi, kan shugabancin da yake gudanarwa. Ga yadda tattaunawar ta kasance:-

    GTK; Mene ne za ka ce dangane da dawowar da shugaban kasa Muhammad Buhari ya yi daga jinyar da ya tafi kasar Ingila?
    Archibishop Kaigama; Muna godiya ga Allah da ya dawo mana da shugaban kasa Muhammad Buhari gida lafiya, bayan jinyar da ya je. Muhammad Buhari shi ne shugaban Nijeriya kuma addininmu na kirista ya nuna mana cewa mu rika yiwa shugabanni addu\’a. Mu yi masu addu\’a  don su sami koshashiyar lafiya, mu yi masu addu\’a don Allah ya ba su hikimar yadda za su gudanar da harkokin mulkin jama\’a domin jama\’ar su sami jin dadi da ci gaba.
    Ko mun so ko mun ki shugaba Buhari shi ne shugaban  Nijeriya, don haka dole mu yi masa addu\’a dole ne mu yi masa fatan alheri. Dalilin haka duk masu tunani, ba za su yi wa shugaban kasa Muhammad  mummunan fata ba. Za su yi masa fatan alheri da addu\’ar Allah ya ba shi lafiya.
    Idan shugaban kasa ya yi rashin lafiya dole  mu damu, dole  mu sunkuya mu durkusa mu daga hannu sama mu yi masa addu\’a mu roki Allah ya ba shi lafiya. Dukkanmu zamu iya fadawa cikin ciwo mu yi rashin lafiya.

    GTKI; To maye za ka ce kan maganganun da wasu suka yi tayi kan wannan rashin lafiya da shugaban kasa ya yi?
    Archibishop Kaigama; A gaskiya na yi matukar bakin ciki kan yadda naji wasu \’yan Nijeriya suna cewa shugaban kasa  ya zauna a  wajen jinyar da ya tafi,  ko kuma ya mutu a can.  Masu irin wadannan maganganu
    mutane ne wadanda za mu iya cewa ba masu hankali ba ne. Kuma ina jin ba cikakkun masu bin addini  ba ne.
    Kamar yadda na fada shugaba, shugaba ne kuma Allah ne ya nufa mu sami shugaban  da zai ceto kasar nan, wannan shugaban kuwa shi ne shugaba Muhammad Buhari. Ko mutum yana  son sa ko baya  son sa shi ne shugaban Nijeriya. Don haka hada kai za mu yi, mu ba shi cikakken goya baya da hadin kai.
    Saboda haka ina kira ga masu yi wa shugaban qasa Muhammad Buhari
    mummunan fata su sake tunani. Domin duk dan adam da yake cikin damuwa ya cancanci a taimaka masa. Balle kuma a ce  shugaban kasarmu gabaki daya.
    To ina irin wadannan mutane  masu yi wa shugaban kasa mummunar fata  suke? ga shi Allah bai karbi mummunan fatar su ba.  Maimakon haka Allah ya ba shi lafiya ya dawo gida Nijeriya, zai ci gaba da gudanar da
    mulkinsa.
    Muna fatar Allah ya kara masa koshin lafiya ya taimake shi ya ci nasara a cikin mulkinsa. Kuma yadda mutane suke cikin wahala muna fatar shugaban kasa ya nemi hanyoyin da zai magance wadannan matsaloli.

    GTK; To  a nan wadanne shawarwari ne za ka bai wa shugaban kasar kan yadda yake shugabancin kasar nan?

    Archibishop Kaigama; Ya ci gaba da aiki da tsoran Allah kuma ya rika sauraron jama\’a kuma ya tabbatar cewa a cikin sha\’anin gudanar da mulki akwai masu son shugaba akwai kuma wadanda ba sa son shugaba. Kada ya damu da wannan ya ci gaba da gudanar da aikinsa tsakani da Allah.
    Wadansu \’yan Nijeriya suna nuna damuwarsu cewa shugaban kasa Muhammad Buhari musulmi ne. Don haka yana son ya mayar da Nijeriya kasar musulmi, wannan ba abin da muka san shugaba Muhammad Buhari da shi ba ne.
    Domin tun kafin ya zama shugaban Nijeriya mu shugabannin darikar Katolika na Nijeriya,  mun yi zama da shi a Abuja mun tattauna da shi. Kuma bayan da ya zama shugaban Nijeriya mun same shi mun yi zama da shi, kuma bai nuna mana yana da irin wannan tunani ba. Don haka muna kira ga irin wadannan mutane kada su ji tsoro domin shugaba Buhari ya zo ne domin ya shugabanci dukkan al\’ummar Nijeriya ne musulmi da kirista da ma masu bin addinin gargajiya.
    Bayan haka Shawarwarina ga shugaban kasa shi ne ya natsu ya bude idanunsa da kunnuwansa domin yaga  abubuwan da suke faruwa ga jama\’a kuma ya ji abubuwan da jama\’a suke fada domin  ya taimaki mutanen
    kasar nan. Domin mutane suna cikin wahalar yunwa da wahalar rashin kudi.
    Shugaban kasa ya lura da wadanda suke kusa da shi. Idan wadanda suke kusa da shi suka bashi shawara ya tabbatar ya nemi shawarar wasu na waje, kafin ya yi amfani da shawara da wadanda suke kusa da shi suka
    ba shi. Domin wani lokaci akwai son kai da son zuciya da siyasa  a cikin shawarar da wadanda suke kusa da shi suke ba shi. Wani yana son kansa da iyalinsa da kabilarsa  ne kawai. Ina jin shugaban kasa yana da basirar da zai iya gane irin wadannan masu bashi shawara na kusa da shi.
    Ya bude idanunsa don ya ga wadanda suka iya aiki kuma suke da kwazo da zuciyar yin aiki don jama\’a. Ya lura da wadanda suke son su kwashe dukiyar jama\’a ba. Domin talakawan kasar nan suna cikin wahala. Amma sai ka ga idan an bada wani abu domin a taimakesu sai kaga wani ya je ya zauna a kan wannan abu. Akwai irin wadannan mutane suna nan a cikin wannan gwamnati ta shugaban kasa Muhammad Buhari. Ba irin wadannan mutane muke so a cikin wannan gwamnati ba. Don haka ina kira ga shugaban kasa ya sake duba wannan al\’amari. Ya duba su waye suke aiki da tsoron Allah kuma su waye suke yi don su cinye dukiyar talakawa da aka ba su.
    Ba maganar wannan daga arewa ko kudu  ko daga wannan addini yake ba. Ba zancen wadannan abokaina ne ba.
    GTK; Mane ne sakonka ga al\’ummar Nijeriya?
    Archubishop Kaigama; Mu ci gaba da yin hakuri duk da cewa muna cikin mawuyacin hali a kasar nan. Kuma mu dogara ga Allah shugabanninmu su san cewa wannan amana da aka basu, suyi abin da ya kamata. Mutane fa sun zave su ne don su je su yi masu jagoranci nagari. Amma wasu da dama sun manta da jama\’ar da suka zabe su. Don haka ina kira ga shugabanni su rika gudanar da ayyukansu da gaskiya da tsoron Allah. Sauran
    al\’ummar kasa suma su zauna cikin tsoron Allah domin idan da musulmi da kirista muna bin abubuwan da addinan namu suka koyar. Ba za mu ji ana kwashe kudaden jama\’a da satar mutane da sauran miyagun abubuwa ba. Kowa ya tashi ya yi aiki tsakani da Allah. Kada mu zuba wa shugaban kasa  ido shi kadai, muma mu tashi mu bada tamu gudunmawar wajen gyara kasarmu Nijeriya.  Mu ba shugaban kasa goyan baya da hadin kai kada mu rika zancen kabila ko arewa ko kudu ko zancen addini.

    LEAVE A REPLY

    Please enter your comment!
    Please enter your name here