\’Yan Majalisa Sun Ja Daga Da Shugaban Kwastam

1
1369

Rabo Haladu Daga Kaduna

CE-CE-KU-CE tsakanin shugaban Hukumar fasa Kauri ta Najeria wato Kwastam, Kanar Hameed Ali mai ritaya, da kuma Majalisar Dattawan Kasa ya ta\’azzara a ranar Talata, bayan da Kanar Hameed ya ce ba zai amsa gayyatar da majalisar ta yi masa ba.
A wata wasikar da Kanal Hameed Ali ya aikewa majalisar, wadda akawun majalisar ya karanta a zauren, shugaban kwastam ya ce ba zai samu damar zuwa ba a ranar Laraba, domin wata ganawar da hukumarsa ta shirya yi daban a ranar.
Shugaban masu rinjaye a majalisar, Sanata Ahmed Lawal, ya ce ba su gamsu da uzurin shugaban hukumar kwastam din ba, yana mai kiransa da ya bayyana a gaban majalisar ranar Alhamis
Sanata James Manager ya ce yin irin hakan cin mutuncin majalisar ne, ya kuma kara da cewa Kanal Ali bai gabatar da wasikar yadda ya dace ba.
Daga karshe majalisar ta umurci Kanar Ali ya bayyana a gabanta yau Laraba da misalin karfe 10:30 na safe.
An dai fara takun saka tsakanin shugaban hukumar ne da majalisar dattawan Najeriya bayan da hukumar Kwastam ta ce dole mutane su biya kudin harajin shigowa da motoci, abin da mafi yawan \’yan majalisar suka kalubalanta.
\’Yan majalisar sun kuma ce lallai sai shugaban Kwastam din ya bayyana sanya kakin aikin hukumar a yayin da zai je gabansu.
Yanzu dai za a zura ido ne zuwa nan ranar Larabar don ganin ko Kanal Hameed Ali zai bi umurnin majalisar na zuwa gaban nata ko kuma a\’a.

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here