BA NI DA KUDIN GYARAN IDON \’YA TA DA MALAMIN SU YA LALATA – Inji Mahaifinta

0
1000
Daga Usman Nasidi

MAHAIFIN wata dalibar makarantar karamar sakandare mai shekaru 14 wacce malami ya lalata ma ido sanadiyar zuba mata bulala a ido ya koka kan neman a bi masa hakkin sa da kuma taimako don nema mata magani.
Idon Raliya Suleiman na dama ya samu matsala ne lokacin da malaminta ya doketa ta hanyar yin amfani da wani bulala da aka nannade da karfe.
Mahaifinta, Suleiman Umar Kachiya, wani manomi a Kachiya, karamar hukumar Kachiya da ke Jihar Kaduna, ya yi bayanin al’amarin a ranar Litinin a asibitin gyaran ido na kasa, dake Kaduna inda take samun kulawa.
A ranar 23 ga watan Fabrairu mallam Suleiman ya ce malamin, Moses Auta, wanda ya kasance malamin ladabtar da dalibai ya yi amfani da zabori da ke nannade da karafuna gurin dukar ‘yar ta sa.
“Na kai rahoton al’amarin ga hukumar yan sandan Kachia. Shi (malamin) ya kai ta babban asibitin Kachiya, inda aka tura mu zuwa asibitin ido na kasa da ke Kaduna.
“Asibitin idon sunce ruwan idonta ya rigada ya tsiyaye don haka bazata iya gani da idon ba. Maganin da za su iya yi mata kawai shi ne su daidaita kwayar idon daga fadawa cikin kokon kanta da kuma dakatar da tsiyayan da yake yi.” Cewar sa.
A halin da ake ciki, mallam Suleiman ya ce kwararru a wani asibiti mai zaman kansa da ke Kaduna, Thelish Eye Clinic, sun ce za su iya dawo mata da ganinta, “amma sun bukaci a dire masu naira miliyan daya.
“A ina zan zamu miliyan daya? Ko da na siyar da gidana da dukkan amfanin gonana, ba zai kai yawan wannan kudin ba. Yan uwana ne ma suke biyan kudin maganinta a yanzu.
“Ina rokon gwamnatin Jihar Kaduna, yan sanda da sauran hukumomi da masu fada a ji a Najeriya da su taimaka su kawo mana dauki.
“Muna kuma rokon hukuma da ta kwatan mana \’yanci daga malamin da ya fasa ma yata idonta guda daya sannan kuma yake yawo a gari kamar babu abunda ya faru,” ya kara da cewa.
Da take bayanin yadda al’amarin ya faru, Ralia wacce idonta ke lullube da auduga ta bayyana cewa malamin, wanda ke karantar da su darasin kimiyya, ya kira su su 20 a wannan rana wanda suka hada da shugaban dalibai, da su same shi a dakin karatu.
“Ya umarce mu gaba daya da mu yi birgima a kasa, sannan ya fara dukan mu da bulala da aka daure da karafuna.
“Na fada mai cewa bani da lafiya kuma ina da raunuka a baya na, amma ya na ce sai ya doke ni har sai da ya buga mun a idona na dama sannan jini ya fara zuba daga ciki. Sauran dalibai suka fara ihu, amma ya ki daina wa har sai da wata malama ta yi gaggawan dakatar da shi.
“Likitoci sun ce ba zan kara gani da wannan idon ba kuma, har sai an kai ni kasar waje don samun kula na musamman.\”
Kakakin \’yan sandan Jihar Kaduna, Aliyu Usman, ya tabbatar da faruwar al’amarin.
“An kawo rahoton al’amarin ga hukumar \’yan sandan Kachiya kuma a yanzu ana nan ana gudanar da bincike,” cewar Mista Usman.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here