Najeriya Za Ta Ci Gaba Idan Aka Kawar Da Banbance-Banbance Da Ake Nunawa A Halin Yanzu

0
1083

MUSA MUHAMMAD KUTAMA, Daga Kalaba

TSOHON Gwamnan Jihar Sakkwato, Dokta Alhaji  Attahiru Dalhatu Bafarawa ya bayyana cewa karramawar da Jami’ar Kalaba ta yi wa fitaccen dan siyasar Jihar Sakkwato har wa yau dan kasuwa kuma Jarman Sakkwato Ali Ummarun kwabo A.A. wata alama ce ta kara tabbatar da hadin kan kasa ba tare da nuna wani bangaranci ko banbanci na addini ba kuma abu ne mai kyau.

Alhaji Bafarawa ya furta haka a Kalaba a yayin hira da wakilinmu na kudanci  a harabar filin jirgin saman kasa da kasa da ke Kalaba Jihar Kuros Riba.Da aka tambaye shi ko mai zai ce game da karramawar da Jami’ar Kalaba tayiwa Jarman Sakkwato tsohon Gwamnan ya kada baki ya ce “abu ne mai kyau wannan ya nuna hada kan kasa da al’ummarta kuma ba tare da nuna wani banbanci na kabila ko na harshe ba wannan abu ne na a yaba matuka”inji shi.

Dan siyasar ya ci gaba da cewa “karramawar da aka yi wa Alhaji Ummmarun Kwabo Jarman Sakkwato ba ta zo masu da mamaki ba matukar idan har wasu da ke waje daya gefe za su ga irin kokari da kwazon gina Jihar Salkkwato da kasa baki daya da ya yi ta fuskar habaka tattalin arzikin kasa da kuma ci gaban al’umma”.

Ya kara da cewa matukar ana son kasar Nijeriya ta ci gaba dole fa sai an kawar da banbancin harshe da na kabila a mayar da kishin kasa da al’ummarta fiye da sauran bukatu.Karshe ya bayyana matukar farin cikinsa da karramawar da aka yi wa dan kasuwar kuma basaraken gargajiya .Yan asalin Jihar Sakkwato mazauna Kuros Riba sun cika makil a harabar jami’ar domin taya dan uwansu murnar karrama shi da aka yi.

Shi dai Ummarun  kwabo A.A.  Jami’ar Kalaba ta karrama shi da digirin girmamawa na mashahurin dan kasuwa da ya bayar da gudunmawa ta bunkasa  harkoki na kasuwanci ita ma tsangayar karatun lauya ta Jami’ar  ta ba shi digirin girmamawa na lauya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here