Daga Usman Nasidi
MAJALISAR dattawan Najeriya ta fada wa shugaban hukumar Kastan Hameed Ali ya tafi kuma ya sake bayyana sanye da yunifam a ranan Laraba, 22 ga watan Maris.
Ba da dadewa ba Hameed Ali ya bayyana gaban sanatocin cikin kaya gida a yau Alhamis kuma sun tuhumce sa a kan rashin biyayya ga majalisa.
Hameed Ali ya ce shi dai bai san wani wuri a doka inda ya wajabta masa sanya yunifam ba amma yana ci gaba da tuntuban lauyoyi.
Amma Sanatoci ba su amince da wannan magana tashi ba yayin da wani sanata Magnus Abe ke kokarin lallashinsa ya sanye yunifam, sauran sanatoci suka yi ca.
Sanata George Sekibo ya bada shawaran cewa a kori Hameed Ali daga cikin majalisa kuma an sanya masa wani ranan ya sake zuwa sanye da yunifam.
Kana kuma Sanata Barnabas Gemade wanda ya goyi bayan wannan shawara ya ce ya kamata Hameed Ali ya nuna hali mai kyau saboda sauran \’yan majalisar su fahimce shi sosai ko a yi masa sassauci.