Gwamnatin Buhari Ce Ta Yi Daidai Da Mutanen Nijeriya-Tambaya Mato

0
955
Isah  Ahmed, Jos
WANI wanda ya yi takarar gwamnan Jihar Filato  karkashin jam\’iyyar PDP
a zaben shekara ta 2007 Injiniya Tambaya Mato ya bayyana cewa
gwamnatin shugaban kasa Muhammad Buhari ce ta yi daidai da mutanen
Nijeriya. Injiniya Tambaya Mato ya bayyana haka ne a lokacin da yake
zantawa da wakilinmu.
Ya ce a gaskiya wannan gwamnati ta shugaban kasa Muhammad Buhari ta yi
daidai da mutanen Nijeriya. Domin mafiya yawan \’yan  Nijeriya ba sa
son aiki, ba sa son wanda yake yin abu mai kyau.
Injiniya Tambaya Mato ya yi bayanin cewa  idan ba irin gwamnatin
Buhari ba, za a ci gaba da samun matsaloli a Nijeriya. Domin ba a taba
samun gwamnatin da ta fito take kama  barayin kasar nan kamar wannan
gwamnati ta Buhari ba.
Ya ce babu shakka wannan gwamnati tazo don gyara abubuwan da aka
lalata a kasar nan a zamanin gwamnatocin da suka gabata.
\’\’Wannan gwamnati ta Buhari gwamnati  ce mai kyau kuma ta fara samun
nasarori a Nijeriya, don haka mu  muna tare da  ita muna goyon bayan
abubuwan da take yi, muna  kira kan ta cigaba da abubuwan da ta sanya
a gaba\’\’.
Ya yabawa gwamnatin kan shirinta na komawa gona a kasar nan. Ya ce
wannan shiri yana da kyau domin duk wani dan Nijeriya da yake son
kansa da kwanciyar hankali to ya koma aikin noma.
Ya yi kira ga Gwamnati ta fito da taki ta baiwa talakawa kan farashi
mai rahusa domin su yi noma. Ya ce idan aka yi shekaru biyu ana irin
noman da aka yi bana  a Nijeriya, za a sami dukkan abin da ake nema.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here