APC Za Ta Shiga Tsakanin Hameed Ali Da Majalisa

  0
  857

  Rabo Haladu Daga Kaduna

  JAM\’IYYAR APC mai mulki  ta ce  za ta shiga tsakanin majalisar dattawa da shugaban hukumar hana fasa kwaurin , wato Kwastan, Kanar Hameed Ali mai ritaya, kan takaddamar da ke tsakaninsu.
  Wata sanarwar da kakakin jami\’iyyar, Bolaji Abdullahi, ya saka wa hannu, ta ce a da jami\’yyar tana bin ce-ce-ku-cen da ta kaure tsakanin bangarorin biyu da tunanin cewar za warware lafiya.
  Sanarwar ta ce yanzu jam\’iyyar tana ganin ya kamata ta shiga tsakani inda ta ce shugaban jam\’iyyar, John Odigie-Oyegun, zai jagoranci wata tawagar sulhu zuwa majalisar domin a sasanta tsakanin mambobin jam\’iyyar da ke takaddama da juna.
  Daga farko dai majalisar dattawan ta nemi Hameed Ali ya gurfana a gabanta cikin kayan sarki domin ya yi bayani kan kudin harajin shigar da motoci kasar wanda hukumar kwastam ta ce za ta fara karba daga mutane.
  Hameed Ali bai bayyana a gaban majalisar ranar Larabar da aka nemi ya je majalisar ba. Sai ranar Alhamis din da ya gabata.
  Da ya isa gaban majalisar cikin farin kaya, majalisar ba ta bashi damar magana ba. Sai ta tura shi gida ya dawo ranar Laraba ta wannan makon cikin kayan sarki domin ya kare yunkurin karbar harajin shigar da motoci daga masu motocin da aka riga aka shigar da su kasar.
  Ranar Talata ne tsohon shugaban masu rinjaye a majalisar, Sanata Ali Ndume, ya nemi a bincki shugaban majalisar, Bukola Saraki, kan shigo da mota kasar ba bisa ka\’ida ba, lamarin da ya sa hukumar ta kwastam ta kwace motar.
  Rahotanni na cewa majalisar na yi wa Hameed Ali bita-da-kulli ne saboda kwace motar da ya shugaban majalisar, Bukola Saraki, ya nemi ya shigo da ita kasar ba bisa ka\’ida ba.
  Amma Bukola Saraki ya musanta zargin a wata sanarwa inda ya ce takaddamar shigowa da mota batu ne dake tsakanin dan kwangilar da majalisa ta sa ya sayo motar da kuma hukumar kwastam.
  Majalisar dattawan ta umurci kwamitin da\’arta ya yi bincike kan zargin da ake yi wa Shugaban Majalisar, Bukola Saraki, kan shigo da mota kasar ba bisa ka\’ida ba.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here