BA ZAN BAYYANA A GABAN MAJALISAR DATTAWA BA – Inji Hameed Ali

0
992
Daga Usman Nasidi
SHUGABAN hukumar hana fasa kwauri ta kasa da aka fi sani da suna Kwastan ya bayyana cewa ba zai gurfana gaban majalisar dattawa ba a ranar Laraba 22 ga watan Maris kamar yadda suka umrce shi ba.
Ali ya tabbatar da haka ne a wata ganawa da ya yi da manema labarai a ranar Talata 21 ga watan Maris a garin Abuja.
Hamid Ali ya bayyana dalilansa na kin hallara gaban majalisar da cewa ya samu wani sammaci daga wani lauya da ya shigar da kara gaban kotu, don haka yi wa kotu karan-tsaye ne idan ya gurfana gaban majalisar a gobe, musamman dangane da batun sanya kakin hukumar kwastan wande shi ne batun da ake tuhumarsa a kai a gaban kotun.
Ali ya ce “Duba da shawarwarin da lauyoyi suka ba ni, da kuma bayanai da na samu daga ofishin Babban lauyan gwamnati, ba zan gurfana gaban majalisa a gobe ba, har sai kotu ta yanke hukunci.”
Ali ya ci gaba da bayaninsa, inda ya ce aikin hana fasa kwauri da suke yi ya hana manyan mutane masu shigo da motoci cin karensu babu babbaka, ba tare da biya musu haraji da ya kamace su ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here