KOTU TA HANA HAMEED ALI BAYYANA A GABAN MAJALISA

0
918
Daga Usman Nasidi
BABBAR kotu ta kasa ta dakatar da gayyatar da majalisar dattijai ta yi wa shugaban kwastan, Hameed Ali
Lauyar mai karar ya musanta izinin majalisar dattijai kan yadda shugaban zai gudanar da ayyukar hukumar.
Shugaban hukumar kwastan din, Hameed Ali ba zai bayyana a gaban majalisar dattijai a ranar Talata ba, kama yadda aka sanar bisa wata kara a babban kotu na kasa da ke Abuja, a jiya.
Wannan umurni ya kunshi cikin littafi na sammaci mai lamba FHC / ABJ / CS / 207/2017 wanda lauya Mista Mohammed Ibrahim ya gabatar a gaban kotu jiya.
Mai karar ya bayyana cewa majalisar dattijai ba za ta iya ba Comptroller General na kwastan umurni kan yadda zai gudanar da ayyukar hukumar ba a tsarin mulkin kasa. Shugaban kasa ne kawai ke da izinin ba da wannan umurnin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here