Isah Ahmed, Jos
IMAM Ibrahim Awwal [Usama] Funtua shi ne Limamin masallacin unguwar
\’yan majalisar tarayya da Ke Zone B, Apo a babban birnin tarayya
Abuja.
A wannan tattaunawa da ya yi da wakilinmu kan dambarwar da ke faruwa
tsakanin majalisar dattawa da fadar shugaban Kasa. Kan kin amincewa da
sunan shugaban hukumar EFCC Ibrahim Magu da majalisar tayi da kuma
tilastawa shugaban hukumar kwastan ta Kasa Kanar Hameed Ali ya sanya
kakin hukumar. Ya bayyana cewa majalisar dattawa ta daurewa cin hanci
da rashawa gindi a Nijeriya.
Ga yadda tattaunawar ta kasance
GTK; Mene ne za ka ce dangane da dambarwar da ke faruwa na kin amincewa
da shugaban hukumar EFCC Ibarahim Magu da kuma tilasta wa shugaban
hukumar kwastan ta kasa Kanar Hameed Ali mai ritaya, sanya kakin
kwastan da ‘yan majalisar dattawa suka yi?
Imam Usama; Babban abin da zance kan wannan dambarwa shi ne wani abu
ne na son zuciya. Saboda idan ka dauki shugaban hukumar EFCC, tun da
farko shugaban kasa ya tura sunan wannan mutum don ‘yan majalisar
dattawa su amince amma suka ki.
Ya zo ya sake tura masu sunan wannan mutum a karo na biyu, domin su
amince sun sake kin amincewa da wannan mutum. Kuma kafin ‘yan
majalisar dattawan nan su sake kin amincewa da sunan wannan mutum a
karo na biyu. Akwai wani sanata daga cikin su da suka cire shi daga
kan wani shugabanci da yake rike da shi a majalisa, saboda yana
goyan bayan wannan shugaban hukumar ta EFCC.
Wannan dambarwa da ake yi a majalisar kan Ibrahim Magu wasu ne daga
cikin ‘yan majalisar saboda laifaffukan da suka aikata suke ganin
cewa idan Ibrahim Magu ya sami wannan dama ba zai saurara masu ba.
Wannan dalili shi ne ya kawo wannan dambarwa kan amincewa da shi a
majalisar.
Shi kuma shugaban hukumar kwastan ta kasa Kanar Hameed Ali mai ritaya
da majalisar take maganar cewa dole ne, sai ya sanya kakin hukumar.
Yanzu wannan magana tana gaban kotu kuma masana dokokin kasar nan,
suna ganin cewa babu wata doka da ta tilasta cewa dole sai ya sanya
kakin na hukumar ta kwastan.
Kuma yanzu majalisar nan tana nan, tana bincike kan wasu motoci da
shugaban majalisar ya sayo wadanda aka yi masu takardun kwastan na
bogi. Haka kuma majalisar tana bincike kan wasu abubuwa da suka shafi
Sanata Dino Melaye. Kaga wannan ya nuna cewa saboda Hameed Ali bai
daga masu kafa bane yasa suke wannan abu. Wannan wani babban abin
kunya ne ga Sanatoci a ce suna yin wadannan abubuwa don ba a daga masu
kafa ba.
Akwai wasu shugabanni a baya wadanda suka yi laifaffuka, amma wadannan
Sanatoci basu yi ko mai a kai ba. A lokacin gwamnatin da ta gabata
harin bam na farko a Nijeriya da kungiyar ‘yan tawayen Neja Delta
vangaren Herry Okar suka kai a Abuja, kuma suka fito suka ce su ne suka
aikata. Shugaban kasa na lokacin ya fito ya ce ba su ne suka kai
wannan hari ba. Shi ya san wadanda suka kai wannan hari. Amma a
lokacin ‘yan majalisar ba su cewa shugaban kasar komai ba, kan wannan
katobara da ya yi.
Bayan haka ya kara fitowa ya ce ya san ‘yan boko haram yana cin
abinci da su yana komai tare da su, duk da irin halin da aka shiga a
wancan lokacin, amma ba su ce komai ba.
GTK; Ganin irin wannan dambarwa da take faruwa kan wadannan mutane da
shugaban kasa ya nada, yaya kake ganin dangantakar shugaban kasa da
majalisar dattawa?
Imam Usama; Gaskiyar magana idan aka yi la’akari da wadannan abubuwa
da suke faruwa, dangantakar shugaban kasa da majalisar dattawa bata da
kyau. Lallai ne shugaban kasa ya lura da wannan abu ya yi gyare-gyare
domin ya sami cimma nasarar da yake son ya cimma. Domin a yau a cikin
wadannan ‘yan majalisar dattawa da wuya a sami sama da mutum 10 da
suke tare da shi dari bisa dari. Sai dai saboda tsoro wasu ba za su
iya fitowa fili su bayyana kan su ba.Wadanda kuma suke tare da shi ba
a basu dama suyi magana a majalisar. A yanzu a cikin shugabanin wannan
majalisa akwai wadanda ba dan suna jin tsoron ‘yan Nijeriya ba, zasu
iya fitowa su ce zasu tsige shugaban kasa.
Abin da ya sanya ‘yan majalisar nan suke yin wadannan abubuwa shi ne
mafiya yawa daga cikin su akwai tsofaffin gwamnoni, wasu kuma sun
rike manyan mukamai kuma suna ganin sun yi wasu laifuffuka. Ta yadda
idan suka bada dama aka yi doka wadda za ta hukumta kowa to ba za su
sha ba.
Don haka yanzu a Nijeriya babu inda aka daure wa cin hanci da rashawa
gindi kamar a majalisar dattawan Nijeriya. Don haka muna kira ga
malamai da fastoci su fito su yaKi wannan ta’addanci na cin hanci da
rashawa da majalisar dattawan Nijeriya ta Daure wa gindi.
GTK; To a ganin ka wadanne matakai ne ya kamata shugaban kasa ya
dauka kan wannan al’amari?
Imam Usama; Matakan da ya kamata ya dauka sune ya tabbatar da cewa
kamar yadda aka san shi cewa shi adali ne. To ya tabbatar da cewa duk
kasar nan babu wanda yafi karfin a hukumta shi. Idan har wadanda suka
yi shugabancin kasar nan, za su iya laifi a kamasu a kai su gidan yari.
A yanzu banga wani da ya wuce a hukumta shi ba, a qasar nan.
Amma ace wasu sun fi karfin hukumci a cikin wannan gwamnati wannan shi
ne matsalar. Don haka ko dan da shugaban kasa ya haifa, idan ya
tabbatar mabarnaci ne ya raba shi da matsayin da ya bashi kuma ya
tabbatar an hukumta shi.
Mataki na biyu shi ne duk ma’aikatar da ya san wasu abubuwa suna
faruwa sunki ci sunki cinyewa ya yi kokari ya nemo wadanda suka rike
wannan ma’aikata a baya, ya nemi shawararsu. Idan ya zama mai karbar
shawara in Allah ya yarda za a sami nasara.
GTK; Karshe wanne sako ko kira ne kake da shi zuwa ga al’ummarNijeriya?
Imam Usama; Sakona ga ‘yan Nijeriya shi ne ya kamata su sani cewa ba
zai yiwuwa su zuba ido suna kallo ana yin bubuwa marasa kyau a
Nijeriya ba. Bai kamata a zubawa shugaban kasa ido shi kadai ace shi
ne zai gyara komai a Nijeriya ba. Dole a fito a tallafa masa kan gyara
abubuwan da suka lalace a Nijeriya.
Kuma maganar da shugaban kasa yake yi cewa shi yana bin doka da oda
ne. To ya kamata ya sani cewa a Nijeriya akwai dokar da idan ka
karyata, ya kamata a yi maka kyauta, kan karya wannan doka da ka yi.
Yanzu yadda abubuwa suka lalace a Nijeriya babu yadda za a yi a ce za a
bi doka dari bisa dari. Dole sai an karya wata dokar sannan za a iya
yin wani gyaran.