Saraki Ya Ce Bai Cikin Badakalar Wawushe Naira Biliyan 3.5

    0
    749

    Rabo Haladu Daga Kaduna

    SHUGABAN Majalisar dattawan , Bukola, Saraki ya ce ba shi da hannu a badakalar wawushe naira biliyan 3.5 daga cikin kudaden bashin da kasashen Paris Club suka yafe wa Najeriya.
    Kafofin yada labarai a dai sun bayar da rahotannin yadda wani rahoton hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta\’annati EFCC ya shaida wa shugaban kasa Muhammadu Buhari, cewar Sanata Sarakin ya yi amfani da mataimakin shugaban ma\’aikatansa da kuma wasu jami\’ansa wajen halatta kudin haram.
    Rahotan ya bayyana yadda Mista Saraki ya hada mataimakin shugaban ma\’aikatansa da wadanda suka tuttura kudaden zuwa asusun bankunan da ke da alaka da shi.
    Rahoton na EFCC ya ce za a iya tuhumar shugaban majalisar da wadanda suka taimaka masa da laifin halatta kudin haram.
    Nigeria: Zan yi a-yi-ta-ta-kare da cin hanci da rashawa -Magu
    Bukola Saraki: Ban aikata laifin komai ba
    Amman mai taimaka wa Mista Saraki a kan harkokinyada labara, Yusuph Olaniyonu, ya karyata rahoton, yana mai cewar wani matakin ramakon gayya ne daga mukaddashin shugaban hukumar EFCC, Ibrahim Magu, wanda majalisar dattawan Najeriya ta ki tabbatar da shi a matsayin cikakken shugan EFCC din.
    Rahotanni sun ce yayin da aka mika rahoton badakalar ga shugaba Buhari ranar 10 ga watan Maris, ita kuwa majalisar dattawan ta ki ta tabbatar da Ibrahim Magu a mukaminsa ne ranar 15 ga watan Maris.

    LEAVE A REPLY

    Please enter your comment!
    Please enter your name here