Isah Ahmed, Jos
SHUGABAN majalisar malamai na kungiyar Jama\’atu Izalatil Bid\’ah Wa\’ikamatis Sunnah ta kasa Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir ya bayyana cewa ya zuwa shekarar da ta gabata,kungiyar ta sami nasarar
bude makarantu manya da kanana guda 6,061 wadanda suke dauke da dalibai 6,885,077 a sassa daban-daban na Nijeriya da kasashen waje.
Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi a wajen taron kaddamar da gidauniyar neman gudunmawar Naira Miliyan 175 don sayen motoci da kayayyakin aiki da kungiyar ta gudanar
a babban birnin tarayya Abuja, a ranar Lahadin da ta gabata.
Ya ce a shekarar da ta gabata sun sami nasarorin gudanar da gasar karatun Alkura\’ani ta kasa karo na 20 da taron kara wa juna sani na kasa karo na 23 da tara zakkar kudade da kayayyakin abinci tare da rabawa ga wadanda shari\’ar Musulunci ta ambata da kuma tura rundunar \’yan agajin kungiyar zuwa sansanonin alhazai da filayen jiragen sama
don taimaka wa alhazai a lokacin tafiya aikin Hajji.
Ya ce a wannan taro suna sa ran samun Maira Miliyan 175 don sayen karin kayayyakin aiki na kimiyyar fasahar zamani ta yanar gizo da motocin da kuma sauran kayayyakin aiki.
Sheikh Jingir ya yi kira ga majalisar dattijai da fadar shugaban kasa su daidaita don yi wa al\’ummar kasar nan ayyukan ci gaba.
\’\’Ku guji sanya rigingimun siyasa cikin al\’amuran tafiyar da mulkin kasar nan domin kasar ta tsira, mu talakawan Nijeriya ba ma son mu ji ana rigima tsakanin majalisar tarayya da fadar shugaban kasa\’\’.
Daga nan ya yaba wa gwamnatin shugaban kasa Muhammad Buhari, ya ce babu shakka zuwan wannan gwamnati ta Buhari an sami tsaro a Nijeriya wanda ba mu taba tsammanin cewa za a same shi ba cikin dan kankanin lokaci.
Ya ce bayan haka gwamnatin ta sami nasara a bangaren harkokin noma da bangaren shari\’a da biyan tsofaffin ma\’aikata kudaden fansho da biyan ma\’aikata albashin da suke bi bashi a wasu jihohin kasar nan.
A nasa jawabin babban bako mai jawabi a wajen taron tsohon Gwamnan Jihar Neja, Alhaji Mu\’azu Babangida Aliyu ya yi kira ga al\’ummar Nijeriya su bai wa shugaban kasa Muhammad Buhari goyan baya da hadin kai, domin ya cimma nasarar kudurorin da ya sanya a gaba.
Ya ce shugaban kasa Muhammad Buhari ne kadai shugaban da ya zo da yaki da gurbacewar al\’ummar Nijeriya, don haka lallai akwai bukatar \’yan Nijeriya su ba shi hadin kai da goyan baya.
Alhaji Babangida Aliyu ya yi bayanin cewa ko bayan Buhari ya kamata duk wani da ya zo nan gaba zai zama shugaban kasa a Nijeriya, ya bayyana wa al\’ummar Nijeriya yadda zai yi ya taimaka wajen magance matsalar gurbacewar Nijeriya.
\’\’Ba zagin shugabanni ake yi ba, idan ka zagi shugaba ko ka tsine masa ka tsine wa kanka ne. Don haka a bai wa shugaban kasa Buhari goyan baya, a taya shi da addu\’a\’\’.
Daga nan ya yaba wa kungiyar kan kokarin da take yi na yada ilmi a Nijeriya da kasashe makwafta. Ya ce wannan kokari da take yi yana da matukar amfani ga al\’umma wajen bunkasa ci gaban rayuwarsu.
Shi dai wannan taro wanda ya sami halartar wakilin gwamnonin jihohi da manyan sarakuna da manyan \’yan siyasa da \’yan kungiya da sassa daban-daban na Nijeriya da makwafta. An tara gudunmawar miliyoyin naira.
Rassan kungiyar na jihohin Nijeriya sun bayar da gudunmawar Naira Miliyan 20 a yayin da Gwamnatocin jihohin Sakkwato da Zamfara kowannensu ta bayar Naira Miliyan 10.
Har\’ila yau Gwamnatin Jihar Bauci ta bayar da kyautar sabuwar mota bas toyota ta kudi Naira Miliyan 13 da gudunmawar kudi Naira Miliyan 2. Gwamnatin Jihar Jigawa Naira Miliyan 5 gwamnatin jihar Nasarawa
Naira Miliyan 5 gwamnatin Jihar Yobe Naira Miliyan 3, gwamnatin jihar Barno naira Miliyan 2.
Sauran su ne gwamnan jihar Sakkwato naira miliyan 3, tsohon gwamnan Jihar Sakkwato Sanata Aliyu Magatakarda Wamako Naira Miliyan 2, tsohon Gwamnan Jihar Kano Sanata Rabi\’u Musa Kwankwaso Naira Miliyan 2 da dai sauran su.