MUSA MUHD.KUTAMA Daga kalaba
HUKUMAR gudanarwar kungiyar kwallon kafa Enugu Rangers,da ke Enugu ta bai wa babban mai horas da kungiyar, Imama Amapakabo,wa’adin ya ci wasannin uku ko kuma ya rasa aikin sa.kungiyar Rangers ce ta lashe gasar kofin Premier na gasar kofin na Nijeriya shekarar 2016. wadda har wa yau ta kasa kai bante a gasar wasan cin Nahiyar Afrika da ka yin a bana.
Mai magana da yawun kungiyar Foster Chime, ne ya sanar da daukar matakin ga manema labarai ya ce an dauki matakin ne ganin kungiyar ita ce zakara a gasar Premier ta Nijeriya amma yanzu wankin hula yake neman ya kai kungiyar dare .