Mutum 2 Sun Mutu Da Yawa Sun Jikkata Sakamakon Abinci Mai Guba

0
828

MUSA MUHAMMAD  KUTAMA  Daga Kalaba

AKALLA mutum biyu ne aka ce sun ce ga garinku nan daga cikin al,ummar Oboso ,yankin Mbube ,karamar hukumar Ogoja Jihar Kuros Riba, da ke yankin Niger-Delta na tarayyar Najeriya .Kwamishina  a ma’aikatar kiwon lafiya ta jihar, Dokta  Inyang Asibong ,ce ta sanar da haka ga manema labarai karshen mako.

Ta ce mutum 40 na kwance a babban  asibitin  garin Ogoja mutu kwakwai-rai-kwakwai ana jinyar su sakamakon cin wani gurbataccen kayan abinci . Kwamishiniyar ta karyata jita-jitar da ake bazawa cewa cutar zazzzabin lassa ce ta faru a yankin.

A wata sabuwa kuma gurbataccen kananzir a jihar ya yi sanadin mutuwar mutum biyu yayin da sha bakwai kuma suke kwance a asibitin koyarwa na jami’ar Kalaba suna karbar magani sanadiyyar kuna da suka samu a jikinsu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here