TASHIN BAM A BORNO: WASU JAMI\’AN TSARO 2 SUN RASA RANSU

0
891
Daga Usman Nasidi
Jami’an tsaro sun bakunci lahira sannan kuma wasu su ka jikkata a lokacin da wani bam ya tashi a garin Dikwa da ke Jihar Borno.
A daidai kan hanyar Maiduguri a garin Dikwa ne wani bam ya tashi inda jami’an tsaro har 2 suka ce ga garinku nan. Haka kuma wasu mutane kusan 3 su ka jikkata a yayin da aka taka wani bam da ‘yan Boko-Haram suka dasa.
Wannan mummunan abu ya faru jiya ne a Jihar Borno kamar NAIJ.com ke samun labari. Irin bam din nan na taba-ya-tashi ne ya yi sanadiyyar mutuwar ‘yan kato da gora a garin Dikwa yayin da suka shiga farautar ‘yan Boko-Haram.
Wani dan kato da gorar ya ce wannan abu ya faru ne bayan sun yi nasara kan wasu ‘yan Boko-Haram. A hanyar dawowa ne dai motar su ta fada kan wani bam nan take motar ta tarwatse inda wannan mummunan abu ya faru. Yanzu dai ana can ana jinyar wadanda suka raunata.
Jiya ne kuma shugaban jami’ar NOUN Farfesa Abdallah Uba Adamu ya bayyana cewa Fursunoni ma suna iya karatu a Jami’ar daga gidan yari yanzu ma dai har wani cikinsu ya dawo zai yi Digiri na uku.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here