MIJI YA YI WA \’YAR MATARSA \’YAR WATA 7 FYADE A KATSINA

0
1056
Daga Usman Nasidi
WANI mutum mai shekaru 55 mai suna, Magaji Dansale, ya yi wa yarinya mai watanni 7 da haihuwa fyade a kauyen Marmachi, karamar hukumar Musawa a Jihar Katsina.
Mahaifiyar yarinyar Zeenatu Muntari, ta bayyana wa manema labarai cewa ta rabu da mahaifin yarinyar ne ta auri Dansale.
Mahaifiyar tana mai cewa tana zargin ta sha wani abun da ya sata ta kwashe awanni tana barci har ya samu damar yin lalatar da ya yi.
Game da cewarta da tashinta daga barci ke da wuya domin bai wa yarinyar tata nono, sai ta ga jini a farjin jaririyar.
Ta ce “Da na fada wa mijina sai ya fara kuka; ya ce wasu za su fara tuhumarshi. Da gari ya waye, yayin da nike wanki, sai na ga jini a wandonsa.
“Daga baya sai ya je daji ya kawo min ganye in ba ta, wai basir ne. daga baya muka kai yarinyar asibitin Malumfashi inda Likita ya tabbatar da cewa fyade ne kuma an sanar da \’yan sanda.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here