Ta Zargi Tsofaffin Gwamnoni Da Hana Ruwa Gudu A Mulkin Najeriya

0
872

 

 

MUSA MUHAMMAD KUTAMA Daga  Kalaba

KUNGIYAR matasan Nijeriya masu da’awar son kawo sauyi wadda a Turance aka fi sani da ‘Nigeria youths for positive change’ cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar kwamared Nasir Kabir ya bai wa Gaskiya Ta Fi Kwabo yau Juma’a  a Kalaba lokacin da suka gudanar da gangami na shiyyar kudu maso kudu y ace, kungiyar  ta zargi daukacin Gwamnonin tarayyar Nijeriya da yin babakere da handame kason kudaden kananan hukumin Nijeriya 774. Suna yin wandaka da su alhali lalitocin kananan hukumomin an bar su fanko.

Sanarwar mai dauke da sanya hannun shugabanta na kasa Kwamared Nasir Kabir ta ci gaba da zargin Gwamnonin da cewa da zarar Gwamna ya gama wa’adin mulkin jiharsa na tsawon shekara 8 ya kwashe kudaden karamar hukumar jiharsa ya hana ta sakat ya gaza biyan albashi ya tafi ya bar magajina da dimbin bashi sai ka ga sun koma takarar kujerar majalisun tarayya domin sun tsallake siradin binciken yin badakala da kudin karamar hukuma.

Sanarwar ta ci gaba da cewa tsaffin gwamnonin da suka handame kudaden kananan hukumomin jihohin su suna ci gaba da zama alakakai da alkalai saboda rigar kariya da suke fama da ita a jikin su bayan sun zama Sanata ko dan majalisar wakilai sun tsallake duk wani shinge na gurfana gaban kotu.NYPC ta kara da cewa  suna tursasa wa talakawa shugaban karamar hukumar da  ran su yake so ba wanda talakawa suke so su zaba ba bugu da kari ma su ne suke dora duk wani wanda zai yi takarar majalisar dokokin jiha,kana kuma su ne kanwa uwar gamin a wajen ware wanda ya cancanta ya zama dan takarar mukamin  shugaban kasa .

Kungiyar matasan masu son kawo canji a kasa sun ci gaba da zargin tsaffin gwamnonin da sai wanda suke so shi zai zama alkali a kowace kotu ta kasar nan matukar suka san wancan ba zai tava zama dan amshin shatan su ba  ba za su taba bari ya zama alkali ba. Haka zancen ma yake a nada ministoci da shugabannin hukumomin zabe tun daga matakina jiha zuwa na tarayya hatta ma daraktocin kamfanoni da ma’aikatun gwamnati sai dan lelen su.inji kungiyar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here