Mun Hada Musabakar Alkur’ani Don Zaburar Da ‘Ya’yayenmu Sanin Littafin Allah – Manjo Sa’ad

0
1034

MUSA MUHAMMAD KUTAMA Daga Kalaba

AN gudanar ka masabakar karatun Alkur’ani mai tsarki a barakin soja da ke runduna ta 13 hedkwata Kalaba Jihar Kuros Riba.Makasudun shirya gasar kamar yadda babbann limamin masallacin brigade ta 13 Manjo Kabiru sa’ad Yakubu ya shaidawa wakilinmu shi ne domin su dada zaburar da ‘ya’yansu karatun Alkur’ani da kuma sanin sauran bangarori da suke wajibi da al’ummar musulmi su sani su ma su sami ilimi domin su san hakan “saboda daga abin da Allah ya sa na lura a karatun Alkur’ani akwai ci baya sosai yanzu ,al,umma sun fifita karatun boko fiye da na addini wato na Alkur’ani, kuma karatun Alkur’ani  da hadisin manzo s.a.w.shine musulunci kuma shine rayuwar mutum musulmi saboda haka idan yasan komai shi ne za ka ga yana kamanta komai  na ga ilimi na ci baya musamman karatun Kur’ani na ci baya shin ya sa na ce bari in yi kokari in hada wannan masabaka”inji  shi.

Babban limamin wanda har ila yau shi ne shugaban kungiyar limamai da alarammomi ta Jihar Kuros Riba ya ci gaba da cewa  ya matsa kaimi kan hakan ne domin ya jawo hankalin iyaye musamman masu rauni wajen kula da karantar da ‘ya’yan Alkur’ani da Hadisan Annabi da kuma yara da suke son zuwa islamiyya amma iyayen suna hana masu zuwa “wannan shi ne dalili na hada wannan masabaka kuma in sha Allah kwanan nan za mu hada ta jiha baki daya”inji Manjo Sa’ad .

Da yake karin haske game da hada masabakar ta matakin jiha, shugaban kungiyar limamai da alarammomi ta Kuros Riba ya ce za su tantance dalibai ne domin shiga gasar masabakar karatun Alkur’ani ta kasa da ake yi ko wace shekara “mu ma da yardar Allah an daina barin Jihar Kuros Riba baya wajen shiga gasar masabakar daga cikin dalibai da suka yi fice za mu mika sunayen su su wakilci al’ummar musulmin Kuros riba wajen masabar idan Allah ya kaimu lokacin”.Bataliyar  soja hudu ce a karkashin birged ta 13 mai hedkwata Kalaba da suka hada da runduna ta 130.da ke Ogoja da 146. Eburutu ,da ke nan Kalaba .Sauran su ne 93.da ke Takum jihar Taraba da 245.Ikom.

Karshe ya bayyana gamsuwarsa da masabakar domin kuwa kwalliya ta biya kudin sabulunta “Alhamdulillahi kwalliya ta biya kudin sabulunta”.Ya gode wa daukacin duk wadanda suka bada gudunmawa wajen samun nasarra kammala masabar cikin nasara.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here