Isah Ahmed, Jos Da Usman Naasidi Daga Kaduna
A yau ne dubban daruruwan mutane suka yi jana\’izar fitaccen malamin addinin musuluncin nan da ke zaune a
garin Jos, kuma jigo a kungiyar Jama\’atu Izalatil Bad\’ah Wa\’ikamatis sunnah ta kasa Sheikh Alhassan Sa\’eed Adam Jos bayan da Allah Ya karbi rayuwarsa jiya Laraba da yamma.
Shi dai marigayi Sheikh Alhassan Sa\’eed Adam Jos ya rasu ne a wani asibiti a Kano bayan da ya je don a duba lafiyarsa a wannan rana ta Laraba.
Ya rasu ya bar matan aure 4 da \’yaya maza da mata 26 da jikoki da dama.
An haife marigayin a garin Mikeke da ke karamar hukumar Gumel a jihar Jigawa shekaru 59 da suka gabata.
Ya yi karatu a jami\’ar Madina da jami\’ar Usman Danfodio da ke Sakkwato da jami\’ar Jos.
Kafin rasuwarsa shi ne na\’ibin babban malami mai tafsirin watan azumin Ramadan a masallacin sultan Bello da ke Kaduna. Har\’ila yau kuma shi ne shugaban fatawa na kungiyar Jama\’atu Nasril Islam reshen Jihar Filato.
Top of Form |
Bottom of Form
Top of Form
Bottom of Form