Ba Saɓon Allah Ne Ya Jawo Sankarau Ba — Sarkin Kano Sanusi

0
8009

Rabo Haladu Daga Kaduna

MAI martaba Sarki Kano Muhammadu Sanusi II ya soki Gwamnan Jihar Zamfara Abdul\’aziz Yari a kan kalaman da ya yi cewa sabon Allah ne ya haddasa cutar sankarau a jiharsa.
Da yake jawabi a wurin wani taro kan zuba jari da aka yi a Kaduna, Sarki Sanusi ya ce bai kamata mutum mai mukami irin na Gwamna ya rika alakanta abin da ya shafi kiwon lafiya da sabon Allah ba.
A cewarsa, \”Mutum sama da 200 sun mutu, an tambayi Gwamna amma ya ce wai sabon Allah ne ya sanya hakan. Bai kamata a rika yin irin wannan jawabi ba. Wannan kalami da {Yari} ya yi bai yi daidai da koyarwar Musulinci ba.\”
\”Idan ba shi da maganin rigakafin sankarau, sai kawai ya je ya nemo\”, in ji mai martaba Sarkin na Kano.
A ranar Talata ne dai Gwamna Abdul\’aziz Yari ya ce saɓon Allah da ake yi ne ya jawo annobar sanƙkarau da ake fama da ita a jihatsar.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da wani jawabi ga manema labarai a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
Ya yi jawabin ne bayan ya yi wata ganawa da shugaban kasar Muhammadu Buhari a kan batun.
Zamfara ce Jihar da annobar ta fi kamari tunda cutar ta barke, inda sama da mutum 200 suka mutu, kuma ake bai wa wasu da dama kulawa a asibitoci da cibiyoyin lafiya.
A makon da ya gabata ne Kungiyar likitoci ta Najeriya reshen jihar, ta soki gwamnatin Zamfaran a kan gazawarta wajen shirya wa barkewar annobar duk da gargadin da aka rika bayarwa.
A hannu guda kuma gwamna Yari ya ce barkewar annobar ba zai rasa nasaba da rashin biyayyar da mutane ke yi wa Allah ba a wannan lokaci.
Ya ce, \”Mutane sun ƙkauracewa Allah kuma ya yi alkawarin cewa idan ka yi ba daidai ba to kuwa zaka ga ba daidai ba, kuma ni dai a iya tunanin na wannan shine dalilin da yasa ake fuskantar wannan annobar\”.
Gwamnan ya kara da cewa babu yadda za a yi a ce zina ta yi yawa kuma Allah ba zai saukar da annobar da babu maganinta ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here