Isah Ahmed, Jos
MAKARANTAR koyar da karatun Alkura\’ani mai girma ta Daibatu Ahbabu da
ke Domawa a karamar hukumar Lere da ke jihar Kaduna ta yi bikin yaye
dalibanta guda 23 da suka sauke karatun Alkura\’ani mai girma a
karshen makon da ya gabata.
Da yake jawabi a wajen bikin mai martaba Sarkin Saminaka Alhaji Musa
Muhammad ya bayyana cewa bude irin wadannan makarantu yana taimakawa
wajen bunkasa duk garin da aka bude su.
Ya ce duk inda gari yake idan babu ilmin addini ba zai sami cigaba
ba. Kuma mutumin da ya yi karantun Alkura\’ani ya gama komai.
Sarkin wanda wazirin Saminaka Alhaji Muhammad Rabi\’u Umar ya wakilta
yi kira ga al\’ummar wannan yanki su cigaba da bude irin wadannan
makarantu.
A nasa jawabin shugaban makarantun Daifatu Ahbabu Rusullilah na kasa
Sheikh Hamza Rijiyar Lemo Kano ya yi kira ga iyaye su kula da
tarbiyar yayansu domin tarbiyar yara da ilminsu shi ne zaman lafiyar
al\’umma. Ya ce hakki ne a kanmu mu baiwa yayanmu tarbiya mai kyau,
domin sune manyan gobe.
Sheikh Hamza Rijiyar Lemo wanda Malam Aliyu Sheikh Hamza Rijiyar
Lemo ya wakilta ya yi bayanin cewa wannan makaranta ta koyar da
karatun Alkura\’ani mai girma wani babban alheri ne ga wannan gari na
Domawa.
Ya yi kira ga al\’ummar garin su tallafawa wannan makaranta domin ta
bunkasa ta cigaba da aikin koyar da yaransu.
Shima a nasa jawabin Sheikh Balarabe Safuwan Saminaka ya bayyana cewa
duk wanda yake karanta Alqura\’ani a ranar tashin Alkiyama Alkura\’anin
zai cece shi.
Ya ce babu shakka alheri zai sauka a wannan gari saboda karatun
Alkura\’ani da daliban wannan makaranta suke yi. Don haka ya yi kira ga
iyayen yara da sauran masu hali su taimakawa wannan makaranta.
Tun da farko a nasa jawabin shugaban makarantar ta Daifatu Ahbabu
Rusullilah Domawa Malam Umar Alasan Domawa ya bayyana cewa sun shirya
wannan taro ne domin mu yaye daliban wannan makaranta guda 23 da suka
sauke karatun Alkura\’ani mai girma.
Ya ce sun fara bude wannan makaranta ne da dalibai guda 20 da malamai
guda 2, amma yanzu suna da dalibai sama da guda 400 da malamai 12.
Ya ce wannan makaranta baya ga karatun Alkura\’ani da suke koyarwa suna
koyar hadisai da fikihu da karatun boko.