Shugaba Buhari Ya Kaddamar Da Shirin Farfado Da Tattalin Arzikin Kasa.

0
826

Rabo Haladu Daga Kaduna

SHUGABAN kasa ,Muhammadu Buhari, ya kaddamar da shirin farfadowa da kuma raya tattalin arzikin kasa a fadar gwamnatin da ke birnin Abuja.
Shugaba Buhari ya ce gwamnatinsa na da kudurin mayar da farfado da masana\’antu a Najeriya don ta zama mai dogaro da kanta.
Ya bayyana fatansa kan cewa shirin zai yi kyakkyawan tasiri ga kasar, ya kuma yi kira ga \’yan Najeriyar da su bi diddigin yadda za a aiwatar da shi.
Taron da aka yi na kaddamar da shirin ya samu halartar mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo da shugaban jam\’iyya mai mulki a kasar, John Odigie-Oyegun da shugaban majalisar dattawan kasar, Bukola Saraki da kuma shugaban majalisar wakilan kasa Yakubu Dogara.
Mista Yakubu Dogara ya shaida wa manema labarai cewar ya yi amanna idan aka aiwatar da shirin, tattalin arzikin kasar zai farfado.
Shirin yana da manufofi uku wadanda suka hada farfado da tattalin arzikin kasar, da inganta rayuwar \’yan Najeriya da kuma mayar da tattalin arzikin kasar zakaran gwajin dafi a duniya.
Shirin yana kuma hakon ci gaban tattalin arzikin Najeriya da kashi 2.19 cikin 100 a shekarar 2017, inda ake tsammanin tattalin azikin zai karu da kashi bakwai cikin 100 na ma\’aunin kididdigar tattalin arziki a shekarar 2020.
Har wa yau shirin yana son ya rage hauhawar farashin kayayyaki zuwa digo daya a shekarar 2020, yayin da yake son kara kudin shigar Najeriya daga naira tiriliyan 2.7 a shekarar 2016, zuwa naira tiriliyan 4.7 a shekarar 2020.
Najeriyar dai ta samu karayar tattalin arziki a karon farko cikin shekara 20.
A cikin shekarar 2016 an samu hauhawar farashin kayayyaki a kasar, inda mutane suka shiga cikin halin ha\’ula\’i.
Najeriya kasa ce da ke da dumbin arzikin man fetur da ma\’adinai, sai dai ta fi samun kudin shigarta ne ta hanyar sayar da man fetur din ga kasashen duniya; hakan ya sa galibin kudin shigar da take samu daga waje ke fitowa daga cinikin man.
Tun a shekarar 2015 ne kuma farashin danyen man fetur din ya fara faduwa a kasuwar duniya sakamakon yawan fitar da shi da ake yi, don haka yawan kudaden kasashen wajen da Najeriyar take samu ya ja baya sosai.
Rashin isassun kudaden kasashen waje ma ya jawo kara tabarbarewar al\’amura wajen tsadar kayayyaki, amma a baya-bayan nan babban bankin kasar ya rage farashin dala ya kuma wadata bankuna da ita, inda masu nema ke samu cikin sauki.
Hakan ya sa farashin kayayyaki suka fara saukowa a baya-bayan nan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here