Mustapha Imrana, Daga Kaduna
GWAMNAN Jihar Neja Alhaji Abubakar Sani Bello da ake wa lakabi da Abu Lolo, ya fito fili ya bayyana wa duniya cewa hoton bidiyon da ake yawo da shi a yanar gizo ba shi aka Jefa ba tsohon Gwamnan ne.
Ya bayyana hakan ne lokacin da yake ganawa da kafar yada labarai ta Muryar Amurka inda ya ce ana ta yi masa waya ana tambayarsa saboda Wanda ya rubuta bayani a kan faifan bidiyon ya ce Gwamna bai ce tsohon Gwamna ba.
\”Wannan jifa da ihun ga tsohon Gwamnan kowa zai iya gani an yi shi ne ranar rantsuwa kuma a filin da aka yi rantsuwar don haka ba ni ba ne don dai ba a rubuta tsohon Gwamna ba ne an dai ce gwamna kawai shi ya sa aka yi ta kirana don haka gaskiyar magana ba ni ba ne\”.
Kamar yadda wakilinmu ya ruwaito cewa ya ci karo da wannan bidiyon a yanar gizo a shafin whattsapp Kuma yana irin yadda ake ta fama da jama\’ar da suka taru a wajen suna ta fadin kalaman da ba su dace ba, Amma da taimakon jami\’an tsaron da ke tare da tsohon Gwamnan lokacin da jama\’a suka rika jifa sai jami\’an suka rika yin harbi da bindigoginsu a sama cikin iska har dai suka samu nasarar saka tsohon Gwamnan cikin mota.
Tasirin wannan faifan bidiyon ya biyo bayan irin yadda ake samun rahotannin cewa jama\’a sun gauraya da wasu Sanatocin ne sakamakon irin takaddamar da ake samu tsakaninsu da bangaren shugaban kasa da ake ganin wata hanya ce da mutane za su magance abin da ba su so da kansu musamman ganin cewa ba ja-ni-in-ja ka suka aika Sanatocin yin jayayya ba musamman da shugaban da suka zaba.