WANI UBA YA TURA YARANSA ALMAJIRANCI DON YA SHAKATA DA AMARYARSA

0
871
Daga Usman Nasidi
WANI bawan Allah a Jihar Kano ya tura yaransa guda biyu almajiranci saboda su ba shi wuri don ya sakata ya wala tare da sabuwar amaryar da ya auro.
Wannan lamari ya faru ne a kauyen Gujungu da ke Jihar Kano inda wannan mutum ya ga ba zai iya zama da yaransa guda biyu ba sakamakon amaryarsa ba za ta saki jiki ta bararraje ba muddin yaran nasa guda 2 na gidan.
Wakilinmu da ya zanta da daya daga cikin yaran yana tambayar shi ko ya ci abinci, inda ya kada baki ya ce “Ban samu abinci ba”, da ya sake tambayarsa ina dan uwansa yake? Sai ya ce “Baya nan, ya je neman abinci.”
Majiyar ta garzaya wajen wani babban malami a Jihar Kano, Sheikh Ibrahim Khaleel wanda ya ce idan wannan batu ya tabbata, to ya zama wajibi hukumar Hisbah ta nemo uban yaran nan don a hukunta shi, sakamakon bai dauke su da mutunci ba.
Matsalar almajiranci abu ne da ya addabi al\’ummar Arewacin kasar nan sakamakon yadda ya zama ruwan dare, inda za ka ga an tuta kananan yara da ba su balaga ba Birni da sunan neman karatu, alhali al\’umma gaba daya ta sani yawon barace-barace kawai suke zuwa yi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here