GWAMNA LALONG: JAGARON CI GABAN JIHAR FILATO

  0
  1238
  Isah  Ahmed, Jos
  A shekaru 16 da suka gabata, jihar Filato ta yi kaurin  suna wajen yake-yaken addini da kabilanci  wanda ya yi sanadiyar asarar dubban rayukan al\’umma tare  da dukiyoyi na biliyoyin naira.  Wannan kaurin suna da Jihar Filato ta yi,  ya sanya kowa a ciki da wajen Nijeriya yana tsoran zuwa jihar.
  A wancan lokacin  rikice-rikicen  sun  sanya komai ya lalace a jihar, tun daga kan harkokin kasuwanci da aikin gwamnati da dukkan sauran harkokin yau da kullum.
  Bayanai sun tabbatar da cewa wadannan rikici-rikice  sun taso ne sakamakon irin mulkin danniya da kabilanci  da gwamnatocin  da suka gabata suka gudanar.
  Sakamakon irin addu\’o\’in da al\’ummar jihar suka yi tayi, kan Allah ya kawo masu mafita kan wannan mawuyacin hali da suka shiga. Allah ya kawo masu Gwamna Simon Bako Lalong ya fito takarar gwamnan jihar karkashin jam\’iyyar APC,  a zaben da ya gabata.
  A lokacin da Gwamna Lalong ya fito takarar  yi alkawarin idan al\’ummar jihar suka zabe shi. Zai yi iyakar kokarinsa wajen ganin an sami zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar, ta hanyar tafiya da kowa da kowa  ba tare da nuna kabilanci ko banbancin addini ba.
  Al\’ummar jihar sun fito kwansu da kwarkwatarsu sun zabi Gwamna Lalong, a zaben da ya gabata na shekara ta 2015, duk da wasu manyan \’yan siyasar jihar da suke cikin jam\’iyyar PDP, sun dauka gwamna Lalong ba
  zai iya cin wannan zabe ba.
  Ya zuwa yanzu dai gwamna Lalong ya fara  samun  nasarar cika alkawuran da ya dauka, musamman kan dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar, sakamakon matakan da ya dauka.  Yanzu a jihar kowa yana shiga duk inda yaga dama  batare da wani tsoro ko fargaba ba.
  Babu bangaren da musulmi baya shiga, haka kuma babu bangaren da kirista baya shiga a jihar. Yanzu an sami gagarumin hadin kai a jihar, sakamakon zuwan wannan gwamnati ta Simon Lalong.
  Bayan haka a bangaren ayyukan  raya kasa a jihar, ya zuwa yanzu gwamnatin Lalong ta nisa. Misali kamar a bangaren harkon bunkasa ayyukan noma ganin cewa yanzu  hankalin al\’ummar kasar nan, ya koma
  kan aikin noma don dogaro da kai da samarwa kasar nan kudaden shiga.
  A daminar da ta gabata gwamnatin Lolang ta sayo  tirelolin takin zamani guda  777    da irin dankalin turawa da tumatur na zamani, ta sayar wa da manoman jihar kan farashi mai rahusa.
  Har ila yau gwamnatin Lalong ta sanya hanu  da wani kamfani mai suna Greenlands Intergrated don samar da na\’urorin adana kayayyakin lambu da sarrafa madara a jihar.
  Kan bunkasa harkokin kasuwanci da masana\’antu kuwa, kamar yadda Gwamna Lalong ya yi alkawarin sake gina babbar kasuwar Jos da ta kone. Wadda gwamnatin jihar da ta gabata, tace ba zata gyara  ba. Gwamna Lalong ya
  bai wa wani kamfani aikin  sake gina wannan  kasuwa. Haka kuma ya yunkuro don ganin an kammala aikin tashar sauke kayayyaki ta tudu da ake ginawa a jihar da kuma sake farfado da kamfanin sarrafa kwalabe da ke jihar da kamfanin yin takin zamani na garin Bokkos  da kamfanin sarrafa  masara  da ke Zallaki tare da haxin gwiwar wasu kamfanonin kasashen waje.
  Har ila yau  ganin yadda Gwamna Lalong ya zo ya sami jihar cikin matsalolin rashin biyan albashin ma\’aikatan tare da danne masu hakkokinsu.
  A shekarar da ta gabata ya yi kokarin biyansu albashin watanni 8 da suke bi bashi, tare da karawa ma\’aikata da malaman makarantu  sama dubu 7 girma a wuraren aikinsu.  Kuma  ya biya  \’yan fansho  kudaden
  da suke bi bashi, tare da sanya sunayen tsofaffin ma\’aikatan da suka yi ritaya sama mutum 500, a tsarin biyan \’yan fansho a jihar.
  Hakazalika a  vangaren harkokin ilmi,  a shekarar da ta gabata gwamnatin Lalong  ta gyara makarantu manya da kanana  da dama a jihar. Kuma  ta dauki  malaman makarantun firamare guda 4000  ta raba su a makarantun firamare na jihar.  Ta amince a karawa malamai da ma\’aikatan da suke aiki a makarantu sama da 2000 girma.
  Har\’ila yau gwamnatin Lalong ta sake  farfado da  jami\’ar jihar da ke garin  Bokkos da aka kafa shekaru 10 da suka gabata.  Tun da aka kafa wannan jami\’a ba a taba yaye dalibai ba, saboda sakacin gwamnatin da
  ta gabata. Amma sakamakon gyare gyaren da gwamnatin Lalong ta yi, a kwanakin baya wannan jami\’a tayi bikin yaye dalibanta na farko.
  A kan kiwon lafiya  gwamnatin Lalong ta gyara asibitoci da dama a jihar,  ta yi kokari wajen ganin ta kawar da cutar nan ta zazzabin lassa da ta barke a jihar. Ta sayo motocin daukar marasa lafiya guda
  5 ta raba su a manyan asibitocin garuruwan Barikin Ladi da Mangu da Panshing da Langtang da Shendam.
  A shekarar da ta gabata  gwamnatin Lalong ta kashe kudade har naira miliyan 525,675,690.30 wajen gyara hanyoyin cikin garin Jos da kewaye.
  A kwanakin baya kuma gwamnatin ta Lalong ta bayar da aikin sake gina wasu hanyoyi guda 8, kan kuxi naira biliyan 5 a cikin garin na Jos.
  Haka kuma  ta bayar da aikin hanyoyin Rantya da Wildlife Park zuwa Rafiki Junction zuwa Miangu Junction da hanyar zuwa jami\’ar jihar  da ke Bokkos zuwa Dokan Kasuwa da ke Shendam kan kudi naira biliyan
  3,980,969,215.78
  Har\’ila yau gwamnatin ta bayar da kwangilar gyara hanyoyi guda 16 a wurare daban daban na jihar.
  A bangaren kasa da tsara birane  gwamnatin Lalong ta samar da filayen gina masana\’antu a jihar,  tare da  rage kashi 50 bisa 100 na kudaden yin rijistar filaye da gidaje a jihar.
  Haka kuma kan  bunkasa harkokin rayuwar mata da jin dadin jama\’a gwamnatin Lalong ta yi abubuwa da dama a shekarar da ta gabata. A inda ma\’aikatar mata ta jihar ta horar da daruruwan mata da matasa da suka fito daga dukkan kananan hukumomin jihar 17,  sana\’o\’in dinki da saka da yin sabulai da kitso da sarrafa na\’urar kwanfuta  da dai sauransu.
  Gwamnatin Lalong ta yi kokari wajen magance matsalar ruwan sha da aka yi shekara da shekaru ana fama da shi a garin Jos da kewaye.  Ta hanyar gyara bututan bada ruwan da suka lalace.
  Haka kuma ta bayar da aikin haka rijiyoyin burtsatse guda 340 a kananan hukumomin Riyom da Shendam tare da biyan kudaden magungunan da za a rika sanyawa a ruwan da ake bai wa al\’ummar jihar, har na tsawon shekara 4.
  Hakazalika an  gyara wutar lantarki na garuruwan Miago da Datti-Zawan da Kung-Bwana da Du da Koran-Foron.
  A bangaren samar da gidaje da raya birane, gwamnatin Lalong ta kammala aikin gyara gidan masaukin baki na gwamnatin jihar  da ke Asokoro a babban birnin tarayya Abuja wanda ta gada daga gwamnatin da ta gabata.
  Kuma ta ware  wani babban fili mai fadin eka biyar, don aikin gina gidaje na tarayya. Tuni ta biya diya ga wadanda suke da wannan fili. Za ta gina rukunan gidaje guda 22,500 a jihar. Tare kuma da wasu  gina rukunan gidaje guda 7,500 a yankunan mazabun sanatoci guda uku na jihar.
  Gwamnatin Lolang tuni ta sanya dokar ta baci, kan tsaftace muhalli a jihar.  A wannan shiri an tsaftace garin Jos da kewaye ta hanyar kwashe dukkan sharar da aka jibge a wurare daban daban na garin Jos da kewaye.  Kuma an sake dawo da yin shara a kowanne karshen wata.
  Gwamnatin ta Lalong ta yi namijin kokari wajen farfado da yawon bude idanu a jihar.  Tuni  ta kulla yarjejeniya da wani kamfani da ke kasar China, mai suna One Belt One Road  don farfado da wasu wuraren
  shakatawa guda biyar a jihar.
  Wuraren shakatawar da aka kullu wannan yarjejeniya a kansu, sun hada da babban otal din nan da ke hanyar sabon asibitin koyarwa na jami\’ar Jos [JUTH] wanda ya yi shekara da shekaru ba a gama aikin gininsa ba.
  Da  tsohon otal din nan na Hill station, da otel Plateau Hotel da gidan ajiye namun daji da ke garin Jos da kuma  gidan shakatawa na Solomon Lar Amusement Park.
  A wannan yarjejeniya da aka kulla kan farfado da wadannan  wuraren shakatawa. Kamfanin zai zo da kudadensa da kayayyakin aikinsa ya gyara wadannan wurare ya mayar da su kamar na zamani. Ya rike su na wasu shekaru daga nan ya dawo wa da gwamnatin jihar Filato, wadannan wurare.
  Kan irin wadannan nasarori da gwamnatin lalong ta samu a  wannan dan kankanin lokaci, baya ga irin ayyukan raya kasa da ta kuduri aiwatarwa a kasafin kudinta na wannan shekara ta 2017.  A ganina Gwamna Samon Bako Lalong ya zama jagoran ci gaban jihar Filato.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here