Daga Usman Nasid
\’YAN sanda sun sha alwashin kara gurfanar da wani Abubakar, mai siyar da shayi a Ngwayanma, dake yankin Kontagora na jihar Neja, bayan an yanke mashi hukuncin wata daya a gidan yari da kuma cin tarar sa na naira dubu talatin (N30,000) sakamakon yima wani yaro, Aminu mai shekaru 12 fyade.
Wannan hukunci na zuwa ne bayan wanda abun ya afku a kansa ya mutu a wani asibiti cikin makon da ya gabata.
An bayyana cewa Abubakar, wanda ake kira da mai shayi, ya sace yaron ne daga iyayensa a watan Maris sannan kuma yayi luwadi da shi a kai a kai na tsawon makonni biyu har sai wani makwabcin sa da ya hankalta ya nemi doki.
A lokacin da \’yan sanda suka zo kama Abubakar, sai suka gano cewa yaron na cikin matsanacin lafiya. A take aka yi gaggawar kai shi asibiti inda ya mutu bayan wasu kwanaki.
Da yake bayanin al’amarin, wani mazaunin yankin ya ce \”Iyayen yaron sun lura da cewar ba sa ganin yaron don haka suka nemi sanin inda yake a wajen abokansa, wanda suka ce ba su san inda yake ba. Bayan nan, aka sanar ma \’yan sanda batun batan nasa. A farkon watan Maris kenan.
\”Bayan makonni biyu, wani mutumi ya sanar mana da cewa ya ga Aminu tare da Mai shayi (Abubakar). Da farko ya karyata cewar yaron na tare da shi. Daga baya aka gano yaron a dakinsa cikin wani mawuyacin hali. Mai shayi ya fadi gaskiyar cewa ya yi luwadi da shi sau da yawa.
\”An kira \’yan sanda don su kama shi sannan aka kai Aminu asibiti. Amma abun bakin ciki shi ne yaron ya rasu a makon da ya gabata Wanda hakan ya sa iyayen ba za su iya cewa komai ba a kan al’amarin a yanzu; domin suna cikin wani irin hali.\”
Jami’in kula da huldar jama’a na hukumar \’yan sandan jihar, DSP Elkana James, wanda ya tabbatar da al’amarin ya kara da cewa za a gurfanar da Abubakar nan ba da jimawa ba a matsayin wanda ya aikata kisan kai.