MUTUM 1 YA MUTU, 3 SUN JIKKATA A WANI KARON BATTAN KWASTAN DA \’YAN SUMOGAL

0
735
Daga Usman Nasidi
WANI rikici da ya kaure tsakanin jami’an hukumar kula da sufurin kayayyaki, wato kwastan da \’yan sumoga masu safarar kaya ta barauniyar hanya ta yi sanadiyyar raunata mutane 3.
Karan battan ya wakana ne a kan titin Daura zuwa Katsina, inda har an samu wani wanda yana nan rai kakwai mutu kakwai.
Rahotanni sun bayyana cewar jami’an hukumar kwastam sun biyo sawun yan sumogan din ne a daidai kauyen Tuma, hakan ne ya yi sanadiyyar fafatawar.
Shaidun gani da ido sun shaida a majiyarmu cewar jami’an kwastan ne suka sanya shinge a kan hanyar, inda suka bude wuta a kan \’yan sumogan har suka kashe mutum daya.
Wasu shaidun kuma sun bada labara akasin wannan, inda suka ce \’yan sumogan sun yi karo da falwaya ne a kokarinsu na tsere ma jami’an hukumar kwastan.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, kwantrolan hukumar kwastan na Jihar Katsina/Kaduna Mohammad Tanko ya ce “Yan Sumogan sun rude ne bayan jami’an mu sun yi musu kawanya, da haka ne suka fara karo da juna.
“Mun samu nasarar kama \’yan motocin \’yan sumogan guda 7 da ke makare da shinkafa. Kuma mun kai maganar ga \’yan sanda, sa’annan mun aika da wadanda suka jikkata asibiti, amma da zaran sun samu sauki za mu gurfanar da su gaban kotu.” Inji shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here