‘Yan Arewa Ku Zauna Lafiya Inji Gwamnatin Kuros Riba

0
901

MUSA MUHAMMAD KUTAMA, Daga Kalaba

AN kara jaddada muhimmancin zaman lafiya da mutunta juna tsakanin mabiya mabanbantan addinai da kuma harsuna musammman tsakanin mai masauki da bakonsa zaman lafiya na kara dankon zumunta da kaunar juna bugu da kari auratayya ma da ke gudana tsakani.

Mataimaki na musamman kan harkokin addinai Raban Bob ne ya fadi haka yayin da ya ziyarci babban Masallacin Unguwar Hausawa da ke Layin Bagobiri Kalaba, Jihar Kuros Riba.

Ya ce “Na zo ne in kawo maku sakon zaman lafiya tare da kiran ku da a zauna lafiya, a lura da wannan unguwa ta Bagobiri ita ce zuciyar Kalaba musammamn ta harkokin kasuwanci “duk abin da ake nema a Kalaba za ka ji an ce ku je Bagobiri, Unguwar Hausawa, idan albasa ko canjin kudaden kasashen waje kake so ko kuma za ka yi tafiya daga nan Kudanci zuwa Arewacin kasar nan sai a ce je ka Bagobiri can za ka samu mota. Kuma irin yadda ake zaune shekaru aru-aru lafiya da juna wannan ya kara tabbatar wa gwamnati da jama’ar Kuros Riba don haka akwai bukatar mu ji ku kuna zaune lafiya domin idan aka ce ba fata muke yi ba an samu hatsaniya a Bagobiri hankalinmu tashi yake yi”.inji shi.

Da yake yin tsokaci game da rikicin limancin babban masallacin tsakanin Na’iban babban limamin Alhaji Garba Dandalin Turawa Kano, Rabaran Bob ya ci gaba da cewa “ba mu ji dadin irin yadda aka samu rashin jituwa a wannan masallaci ba kan shugabanci musamman tsakanin Na’iban liman biyu don babban limamin ba ya gari mun san musulunci addini ne na zaman lafiya amma sai ga shi daga ofishin Gwamna, shi Gwamnan ya samu labarin matsalar da aka shiga, a kan haka nema ya turoni ya ce in isar maku da sakonsa na a zauna lafiya, idan akwai wata matsala kan addini ko wani malamin da ba a so ne ya yi wa’azi ko fadakarwa to ku sanar wa da shugaban kungiyar limamai da alarammomi ta Jihar Kuros Riba da mataimakinsa Manjo Kabiru sa’ad Yakubu da mataimakinsa M.B Zakariya ko kuma ku sanar wa ofishina idan har abun ya gagara”. Ya kara da jankunnensu da kada irin haka ta sake faruwa.

Mataimakin na musamman kan harkokin addinai ga Gwamnan Kuros Riba, Sanata Farfesa Ben Ayade ya kara da cewa sai da zaman lafiya ne ake iya gudanar da harkokin addini da ma na kasuwanci.Da yake karin haske dan tawagar mataimaki na musammamn din tsohon kwamishinan yada labarai na jihar Patrick Ogar ya ce shi a Sakkwato ya yi rayuwarsa can ma ya yi karatu ya fara aikin gwamnati duk a can ya ce, Hausawa sun fara zama a yankin su Obudu da ke Arewacin Jihar Kuros Riba ne tun wajen 1892 , Hausawa suka fara zuwa Kuros Riba yankin Obudu kuma har yanzu sunana ana auratayya ana zaune lami lafiya don haka kuma da kuke kudancin jiha muna fata za ku dore da wannan zaman lafiya.

Da yake mayar da jawabi ta hanyar sakataren sarkin Hausawa da Fulani na Kalaba Alhaji Salisu Abba Lawal wanda sakatare Alhaji Sha’aban Abdullahi ya karanta ya ce Hausawa tun a 1857,ne Hausawa suka zo Kalaba ainihin sunan Unguwar a wancan lokaci ba Bagobiri ba ne, sunanta Sabon Gari sai bayan sarki Bagobiri Allah ya yi masa rasuwa ne aka sauya sunan unguwar ta koma tana amsa sunansa wato Bagobiri wanda sarakuna da manyan Kalaba na wancan lokaci ne suka sauya mata sunan zuwa nata na yanzu.

Sarkin Hausa-Fulani ya bayar da tabbacin zai ci gaba da yin bakin kokarinsa ya ga zama lafiya tsaknin ‘yan asalin jiha da ‘yan arewa ya ci gaba da wanzuwa. Sannan kuma ya gode wa gwamnatin jiha bisa kulawa da taimakawa ‘yan arewa mazauna jihar da take yi ba gajiyawa kana kuma yadda wannan gwamnati ta zabi dan arewa ta bashi mukamin mataimaki na musamman kan baki daba ‘yan asalin Kuros Riba ba wato Barista Musa Abdullahi Maigoro. Karshe sun mika kokon bararsu ga gwamnati na a rika bai wa musulmin jihar kujerar Makka  (Hajji) kamar yadda Gwamnan da ya sauka ya rika yi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here