A TAFI DAJIN SAMBISA DA MASU CEWA BUHARI YA GAZA WAJEN CETO \’YAN MATAN CHIBOK-IMAM USAMA

    0
    790
    Isah Ahmed, Jos
    IMAM Ibrahim Lawal [Usama] shi ne Limamin masallacin gidajen \’yan majalisar tarayya da ke Zone B Apo a babban birnin tarayya Abuja. A wannan tattaunawa da ya yi da wakilinmu kan cika shekaru uku da sace
    \’yan matan Chibok. Ya bukaci gwamnati ta dauki wadanda suke cewa ta gaza zuwa dajin Sambisa su zauna a wajen,don su ga irin kokarin da gwamnati take yi wajen ceto wadannan yara.
    Ga yadda tattaunawar ta kasance:-
    GTK: Mane ne za ka ce dangane da cika shekara uku da sace \’yan matan nan na Chibok wanda ake ta maganganu a kai?
    Imam Usama: To, ni wannan batu na sace wadannan \’yan mata na Chibok yana ba ni mamaki. Na farko ana maganar wadannan \’yan mata na Chibok, a lokacin da aka sace su  ba a zamanin wannan gwamnati  ba ne. Kuma an san cewa a zamanin gwamnatin da aka sace wadannan yara babu abin da gwamnatin ta iya yi, wajen ceto wadannan yara.
    Kuma da aka zo lokacin zaben shugaban kasa mutanen garin Chibok suka ki zaben wannan gwamnati, suka dauki kuri\’arsu suka zabi gwamnatin da aka sace \’ya\’yansu a lokacin ta. Amma duk da ba su zabi wannan gwamnati ba, a lokacin da shugaban kasa Muhammad Buhari ya zo a karkashin gwamnatinsa an  sami nasara ta hanyarn shiga dajin Sambisa aka samu aka kwato wasu daga cikin wadannan yara.
    Sannan kuma wannan gwamnati ta dauki nauyin karatunsu. Amma don an raina wannan gwamnati yanzu an zo ana cewa wai ta gaza wajen ceto wadannan yara.
    Abin tambaya ga irin wadannan mutane da suke cewa wannan gwamnati ta gaza, wajen ceto wadannan \’yan mata na Chibok, shin \’yan matan Chibok ne kadai \’yan boko haram suka  sace a kasar nan? Matan aure da yara
    kanana nawa \’yan boko haram suka sace  a wannan rikici? Mutane nawa aka hallaka a wannan rikici? Sojoji  da \’yan sanda nawa aka rasa a wannan rikici?.  An kashe dubban mutane  a masallatai da coci a wannan rikici.
    GTK: Ba ka ganin an damu da sace wadannan yara ne don an sace su ne a makaranta?
    Imam Usama: Idan ana maganar cewa an sace \’yan matan Chibok ne a makaranta, dalibai nawa aka diba a makarantu a wannan rikici? Dalibai nawa aka je aka kashe a jami\’ar Bayero da ke Kano?. Ban da wannan an je makarantar kiwon lafiya ta Kano an kashe dalibai. Sannan ga \’yan gudun hijira wadanda aka kona gidajensu a lokacin wannan rikici, wasu sun rasa mazajensu wasu sun rasa \’ya\’yansu. Mene ne aka yi wa irin wadannan mutane? Ko su  ba mutane ba ne, \’yan matan Chibok ne kawai mutane?. Ai raina wannan gwamnati ne a fito ana maganar \’yan matan Chibok kadai, a wannan rikici na boko haram.
    Kamar yadda ake ta maganar \’yan matan Chibok ya kamata a fito da wani tsari da za a bi kadin wadanda suka rasa \’yan uwansu a wannan rikici na boko haram.
    Bayan haka wadansu sun dauki wannan fafutuka ta ceto \’yan matan Chibok kamar wani harkokin kasuwanci, suna amfani da wannan dama suna neman abinci. Ana amfani da wadannan \’yan matan Chibok ana tura wa waje neman taimakon kudi. Wasu kuma suna fakewa da wannan magana don su ci
    mutumcin wannan gwamnati. Ga shi kasar Ingila ta fada a lokacin mulkin Jonathan sun so su shiga dajin nan na Sambisa, su kwaso wadannan yara cikin ruwan sanyi amma gwamnatin ta Jonathan ta ki ba da dama. Mene ne ya sanya wadannan masu fafutuka ba su caccaki gwamnatin Jonathan ba, kan wannan abu da ta yi?.
    To, wannan gwamnati ta shugaban kasa Muhammad Buhari ko yanzu ta sauka ta sami gagarumar nasara musamman kan harkar tsaro.
    GTK: Mene ne mafita kan wannan al\’amari?
    Imam Usama: Mafita shi  ne ya kamata wannan gwamnati ta  bada dama a debi wadanda suke cewa  ta gaza wajen ceto \’yan matan Chibok a tafi da su zuwa dajin Sambisa,domin a ci gaba da yin wannan aiki na ceto
    wadannan \’yan mata tare da su. A ajiye su a dajin su yi kamar wata daya ana yin wannan aiki tare da su, ba wai a debe su a jirgi a yi shawagi da su ba. A nan ne za su iya gano cewa wannan gwamnati ta gaza ko ba ta gaza ba, wajen ceto wadannan yara.
    Amma duk wani da zai tsaya a Abuja yana cewa wai yana fafutukar ceto \’yan matan Chibok yana maganar banza ce.
    GTK: To, a karshe wane sako ko kira  ne kake da shi zuwa ga al\’ummar kasar nan dangane da wannan al\’amari?
    Imam Usama: Ina kira ga sarakunanmu da manyan malamanmu  da fastocinmu
    su fito su yi magana kan wannan al\’amari.  Su fito su gaya wa duniya cewa \’yan matan Chibok din nan ba su kadai ne aka cutar ba a wannan rikici na boko haram.  Akwai dubban mutane da aka rasa a wannan rikici
    musamman a wuraren ibadu. Ya kamata a  bi masallatai da coci coci da wannan rikici ya shafa, a yi rajistar mutanen da aka rasa a wannan rikici,domin a biya diyya.

    LEAVE A REPLY

    Please enter your comment!
    Please enter your name here